Mashigar Hurmuz
-
Jiragen Dakon Man Fetur Na Iran 10 A Sun Shiga Cikin Ruwan Malaysia Don Jigilar Man Fetur
A halin yanzu, jiragen dakon man Fetur na Iran 10 masu ɗauke da tutar Iran suna cikin yankin tashar jiragen ruwa ta gabashin Malaysia (EOPL), kuma suna gudanar da ayyukan jigilar man Fetur daga jirgi zuwa jirgi.
-
Sansanin Khatamul-Anbiya: Babu Wani Jirgin Ruwa Da Zai Iya Wucewa Ta Mashigar Hormuz Ba Tare Da Izinin Iran Ba
Kakakin sansanin Khatam al-Anbiya ya sanar: Babu wani jirgin ruwan kasuwanci ko dakon mai da ya samu dama ko zai sami damar wucewa lafiya ta wannan mashigar ba tare da izini da kulawar sojojin Iran masu ƙarfi ba.
-
A Mashigar Hormuz Jiragen Ruwa 4 Kawai Suka Wuce Daga Jiya Zuwa Yau
Trump a daren Litinin ya nanata cewa mashigar Hormuz a buɗe take kuma sojojin ruwan Amurka suna da cikakken ikonta, amma bayanan Kepler sun nuna raguwar zirga-zirgar jiragen ruwa da ba a taɓa gani ba.
-
Vance: Amurka Za Ta Ci Gaba Da Matsa Lamba Mafi Girma A Kan Iran
"J.D. Vance," mataimakin shugaban Amurka, yayin da ya sanar da ci gaba da matsin lamba na Washington a kan Iran, ya ce Amurka a lokaci guda za ta yi ƙoƙarin sauƙaƙe fitar da man fetur da iskar gas ta mashigar Hormuz gwargwadon iko. Ya kuma nanata cewa batun da ya shafi Iran bai ƙare ba tukuna, kuma Washington za ta yi amfani da kayan aikinta na diflomasiyya, tattalin arziki, da soji.
-
Amurka Jiragen Ruwa Fiye Da 30 Suka Ketare Daga Killacewar Iran Bayan Canja Hanya
Cibiyar sojojin Amurka (CENTCOM) a cikin sanarwarsa ta daren jiya game da yanayin mashigar Hormuz da killacewar ruwa na Iran, ta riya cewa "jiragen ruwa fiye da 30" sun ketare mashigar.
-
CNN: Yarjejeniyar Hormuz Tana Gab Kaiwa Matakin Ƙarshe, Amma Ba Kamar Yadda Trump Ya Ke So Ba
Cibiyar sadarwa ta "CNN" ta ba da rahoton cewa yarjejeniyar da ke gudana ta mashigar Hormuz ba ita ce abin da Donald Trump yake so ba yayin da ta ake gab da kawo karshenta.
-
Iran: Babu Shige Da Ficen Jiragie Ruwa Ta Mashigar Hormuz Matuƙar Amurka Na Ci Gaba Da Hare-haren
Hukumar kula da jiragen ruwa ta Iran ta sanar da dakatar da jigilar kayayyaki ta mashigar Hormuz har sai yanayin tsaro ya daidaita, kuma ta yi nuni da cewa za a sake duba dukkan buƙatun wucewa da bayar da izinin da ya dace da wuri-wuri.
-
Reuters: Oman Ta Gabatar Da Shirin Yanki Ga Iran Don Sarrafa Mashigar Hurmuz Tare
Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya nakalto daga wata majiya a yankin Tekun Farisa rahoton cewa, Oman ta gabatar wa Iran wata shawara, tare da goyon bayan wasu kasashen yankin, don samar da wata hanya ta hadin gwiwa wajen sarrafa mashigar Hurmuz; shirin da bisa gare shi, masu amfani da wannan hanyar ruwa za su biya kuɗin ayyukan jigilar ruwa da yadda suke so.
-
IRGC: Amurkawa Suna Kusantowa Ga Ajalinsu A Kowane Lokaci
Rundunar ruwa ta dakarun juyin musulunci ta sanar da cewa Amurkawa suna kara kusantowa a kowane lokaci zuwa loakcin karshe na kai masu hari.
-
Iran: Ba Za Mu Ja Da Baya Game Da Mashigar Hurmuz Ba
Sojojinmu ba za su ja da baya ko kaɗan game da mashigar Hurmuz ba
-
Iran Ta Gargadi Oman Game Da Hurmuz; Kada Ku Bar Amurka Ta Yi Katsalandan A Mashigar
A daidai lokacin da sa’insar Iran da Amurka ke ƙaruwa game da sarrafa mashigar Hurmuz, Tehran, tare da aika saƙonnin gargadi ga Oman, ta nuna rashin amincewa ga duk wani haɗin kai na Muscat da shirye-shiryen Washington don sarrafa wannan hanyar ruwa mai muhimmanci, kuma ta jaddada wajabcin gudanar da mashigar Hurmuz a cikin haɗin kai da yarjejeniya tsakanin Iran da Oman.
-
PGSA: Ba Ba Shiga Ba Fita Ta Mashigar Hurmuz
Cibiyar Kula da Hanyar Ruwa ta Tekun Farisa ta sanar da cewa: Saboda motsin da ba bisa ka'ida ba na baya-bayan nan na sojojin Amurka a yankin, wucewa ta mashigar Hurmuz ba za ta yiwu ba a halin yanzu.
-
Trump Na Shur-Shure Cikin Rikicin Da Ya Wuce Ƙarfinsa
Mujallar Atlantic: Iraniyawa Sun Wulakanta Trump Sau Da Yawa
Mujallar Atlantic a cikin wani nazari mai taken "Ikon Yaƙi Yana Hannun Iran Kuma Trump Ya Cika Da Rudani Kuma Ya Nutsa Cikin Matsaloli Kuma An Wulakanta Shi," ta rubuta: Ikon yaƙin da ke tsakanin Amurka da Iran a yanzu yana hannun tsarin Iran ne, ba Donald Trump ba, kuma fahimtar juna da aka kulla kwanan nan, hasashe ne kawai da Trump ya kwallafa rai da shi, Iraniyawa sun wulakanta shi sau da yawa.
-
Mashigar Hurmuz: Daga Hanyar Makamashi Zuwa Kayan Aikin Fuskantar Makiya Iran
Yaƙin kwanaki 40 ba wai kawai arangamar soji ce tsakanin Iran da makiya ba; harma ta zama wurin juyi na canza ma'aunin iko a Tekun Farisa da kuma sake fasalin manufar fuskantar makiya a yammacin Asiya.
-
Tattaunawar Da Ta Kasa Tabbatar Da Haƙƙin Iran Da Sharuɗɗan Jagora
Bayyanar Sabbin Sakamakon Raunin Diflomasiyya A Tattaunawar Iran Da Amurka
Ana samun ƙaruwa zirga-zirga a mashigar Hormuz. Adadin zirga-zirga a mashigar Hormuz a ranar 24 ga Yuni ya kai 70, wanda ke nuna ƙaruwa da kashi 105 cikin 100 idan aka kwatanta da ranar da ta gabata. Wannan hauhawar ta faru ne saboda ci gaban aikin cire nakiyoyi da ƙaruwar masu son wucewar jiragen ruwa ta hanyar Oman. Mafi yawan waɗannan ayyukan sun shafi zirga-zirgar kasuwanci tare da wucewar kashi 53, jiragen ruwa masu ƙarancin haɗari sune suka fi yawa a wannan rana.
-
Me Yasa Buɗe Mashigar Hormuz Na Ɗan Lokaci Zai Ceci Trump Daga Ƙunncin Da Yake Ciki?
Ana ta magana game da wata yarjejeniya. Yarjejeniyar da za a buɗe mashigar Hormuz a matsayin wani ɓangare na ɗaukar matakin dakatar da killacewa na ɗan lokaci, domin gudanar da shawarwari a wasu fagage. Amma me yasa wannan mataki ya kasance kuskure ne a aiwatar da shi a halin yanzu?
-
Iran: Ba Zai Yiwu Atrump ya Gana Da Jagora Ba
Laftanar Reza'i: Gudanar Da Mashigar Hurmuz Yana Hannun Iran Ne
Kwamandan Dakarun Juyin Musulunci na Iran a yakin tsaro mai tsarki na shekaru takwas, a cikin wata hira da gidan talabijin na CNN na Amurka ya jaddada cewa: Mashigar Hurmuz mallakar Iran da Oman ce, kuma gudanar da mashigar Hurmuz yana hannunmu ne, don haka za mu karbi kudin kare muhalli da kudin zirga-zirga.
-
Jiragen Ruwa 81 Sun Karya Shirin Trump.. Alkaluma Sun Tona Asirin Gazawar Kawanyar Mashigar Hormuz
Wani bincike na bayanai daga dandalin Marine Traffic, an gano cewa jiragen ruwa 53 ne suka ketare mashigar Hormuz suna masu karya dokar Amurka, wadannan jiragen ko dai sun taso daga tashoshin jiragen ruwa na Iran ko kuma suna tafiya zuwa garesu, ko kuma suna ɗauke da tutar Iran, ciki har da jiragen ruwa 11 da suke cikin jerin takunkumin Amurka.
-
Iran Ta Tsara Yadda Zata Gudanar Da Mashigar Hurmuz
A cikin shirin sabon majalisar, za a biya kuɗin shiga ta mashigar ruwa ta Hurmuz. Kashi 30 cikin 100 na wannan kuɗin shiga za a ware su ne don ƙarfafa sojojin ƙasa da kuma kashi 70 cikin 100 na rayuwar al’umma.
-
Iran: Ku Yi Biyayya Ga Sabon Tsarin Mashigar Hurmuz
Azizi, Shugaban Hukumar Tsaron Kasar Iran ya yi kira ga jiragen ruwa da suke yunkurin tsallake Mashigar Hurmuz da cewa: Ku yi biyayya da sabon tsarin ruwa na Mashigar Hurmuz.
-
Iran: Ta Ɗauki Kawanyar Teku Daga Ɓangaren Amurka A Matsayin Karya Tsagaita Wuta
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran: Kafofin yada labarai da jama'a kada su kula da wasan kafofin yada labarai na abokan gaba.
-
Bidiyon Yadda Jirgin Yaƙin Ruwan Amurka Ya Tsere Daga Mashigar Hurmuz
Wannan faifan bidiyo na nuna yadda babban jirgin ruwan Amurka ya tsere bayan gargadin sojojin ruwa na IRGC daga gabashin mashigar Hormuz. An samu wasu rahotannin da ke cewa an ga wasu jiragen dakon mai guda biyu na Pakistan juya daga wucewa daga mashigar Hormuz.
-
Ƙasashe 7 Sun Ƙi Amincewa Da Taimakawa Wajen Buɗe Mashigar Hurmuz
Jamus da Biritaniya suma sun yi watsi da rokon da Trump yayi a hukumance bayan Faransa, Japan, China, Italiya da Girka suka ƙi amincewa.