28 Yuli 2026 - 23:23
Source: ABNA24
Reuters: Oman Ta Gabatar Da Shirin Yanki Ga Iran Don Sarrafa Mashigar Hurmuz Tare

Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya nakalto daga wata majiya a yankin Tekun Farisa rahoton cewa, Oman ta gabatar wa Iran wata shawara, tare da goyon bayan wasu kasashen yankin, don samar da wata hanya ta hadin gwiwa wajen sarrafa mashigar Hurmuz; shirin da bisa gare shi, masu amfani da wannan hanyar ruwa za su biya kuɗin ayyukan jigilar ruwa da yadda suke so.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya nakalto daga wata majiya mai sani, ya ba da rahoton cewa, Oman ta gabatar wa Iran shawarar samar da wata hanya ta yanki don sarrafa mashigar Hurmuz tare.

Dangane da wannan rahoto, wannan shiri, wanda ke samun goyon bayan wasu kasashen yankin ma, ya jaddada shigar kasashen da abin ya shafa wajen gudanar da wannan hanyar ruwa mai muhimmanci, kuma bisa gare shi, Iran ba za ta ɗauki alhakin sarrafa wannan hanyar ruwa ita kaɗai ba.

A cewar wannan majiya, shawarar Oman an tsara ta ne bisa ga tsarin sarrafa mashigar Malaka; tsarin da a cikinsa, masu amfani da hanyar ruwa, bisa radin kansu, zasu rinka biyan kuɗin ayyukan kula da jirgin ruwa, kare muhalli, da ayyukan bincike da ceto.

An buga wannan rahoto ne a daidai lokacin da Amurka ta dakatar da hare-haren sama a kan Iran na ɗan lokaci, kuma wannan lamari ya ƙara fata na sake farfado da tsarin diflomasiyya da kuma bude hanyar zirga-zirgar ruwa gaba daya a mashigar Hurmuz.

Donald Trump, shugaban Amurka, shi ma ya sanar da cewa, tattaunawa da Iran tana gudana, amma idan tattaunawar ta gaza, akwai yiwuwar sake fara hare-hare.

A lokaci guda, "Abbas Araghchi," ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a cikin tattaunawa da takwarorinsa na Oman da Saudiyya, ya tattauna sabbin abubuwan da ke faruwa a mashigar Hurmuz.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa, Araghchi, a cikin waɗannan tattaunawar, ya jaddada wajabcin ƙarfafa hadin gwiwar yanki, ciyar da diflomasiyyar hadin gwiwa, da kuma kawar da rashin tsaro a mashigar Hurmuz, wanda, a cewar Tehran, ya samo asali ne daga ayyukan Amurka.

………………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha