Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Sakataren Babban Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, Manjo Janar Mohsen Rezaei, a cikin tattaunawarsa da gidan talabijin na Iran, ya ce kwamandan hedkwatar rundunar tsakiya ta Amurka "CENTCOM" yana jagorantar ayyukan fataucin mai, yana mai zarginsa da amfani da sojin UAE.
Rezaei ya ƙara da cewa shugaban Amurka Donald Trump ya koma fataucin mai ta hanyar amfani da "miyagu da ke aiki a ruwan iyakar masarautar Oman."
Martani ga maganganun Trump da ke maimaitawa kan cewa mashigar Hormuz a buɗe take, Rezaei ya ce Washington "tana yin fatauci," yana ƙara da cewa mashigar "tana ƙarƙashin ikon Iran kuma mu ne ke sarrafa ta."
Rezaei ya yi nuni da amfani da jiragen ruwa ƙanana 5 zuwa 6 wajen jigilar mai zuwa manyan jiragen dakon mai, yana cewa sojojin Iran na kai hari kan biyar ko shida daga cikin waɗannan jiragen kowane dare.
Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da bayanan jigilar dokn mai suka fallasa raguwar motsin wucewar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz zuwa mafi ƙarncin mataki cikin fiye da wata biyu, bayan tsanantar hare-hare kan jiragen dakon mai.
………….
Ra'ayinka