Qassam rashen Hamas, sun sanar da cewa mayakansu sun yi wa wani gungun sojojin mamaya na Isra'ila kwanton bauna a yankin "Qayzan al-Najjar" da ke kudancin birnin Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza a yammacin Laraba.
Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya wallafa a yau Juma'a, wani cikakken kididdiga kan mafi girman sakamakon yakin kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi a zirin Gaza, kwanaki 560 bayan fara kai hare-hare daga ranar 7 ga Oktoba, 2023 zuwa 18 ga Afrilu, 2025.