-
Yemen: Saudiyya Ta Kai Hare-Haren Kan Hajjah, Al-Bayda, Sa'dah Da Al-Hudaydah
Sojojin Saudiyya sun kai hari kan wasu biranen da lardunan Yemen ta hare-haren sama da makamai masu linzami, wato Hajjah, Al-Bayda, Sa'dah da Al-Hudaydah.
-
Fars: Iran Ta Gudanar Da Mummunan Ayyukan Kai Hari Da Kare Kai A Hormuz Jiya
Wata majiyar soji ta Iran ta ba da labarin cewa sojojinta cikin sa'o'i 24 da suka gabata sun gudanar da ɗaya daga cikin mummunan ayyukan kai hari da kare kai kan jiragen ruwa da suka keta doka da jiragen Amurka.
-
Hizbullah: Babu 'Yancin Kai Yayin Da Isra’ila Ke Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Tare Da Rashin Ikon Gwamnati Na Kare ‘Yan Kasa
Hizbullah, a cikin wata sanarwa a yayin bikin cika shekaru 83 da 'yancin kai, ta nanata wajibcin haɗin kan ƙasa da kiyaye ikon ƙasa da 'yantar da ƙasar da aka mamaye, tana mai nanata cewa ci gaban mamayar Isra'ila kan sassan Lebanon, da barazana da ƙaura da hare-hare, sun lalata 'yancin kai da ake Magana akai.
-
ABC News: Yanayin Mashigar Hormuz Ya Saba Da Iƙirarin Trump
Tashar Amurka ta ABC News ranar Asabar ta nanata cewa halin da ake ciki a mashigar Hormuz ya saba wa iƙirarin Donald Trump, shugaban Amurka, kan buɗewar wannan mashigar ruwa, masana tsaron teku tare da yin nuni da ƙaruwar hare-hare da raguwar tafiyar jiragen dakon mai, sun sanyawa iƙirarin "cikakken iko" na Washington kan wannan mashigar alamar tambaya?.
-
Matasa A Ƙasashe 20 Na Turai Sun Fito Kan Tituna Don Adawa Da Tsarin Soji, Tsadar Rayuwa Da Rikicin Gidaje
Dubban matasa da ƴan ƙasa na ƙasashen Turai sun fito kan tituna don nuna adawa da ƙaruwar matakan soji, tsadar rayuwa, tabarbarewar harkar gidaje da raguwar zuba jari a ayyukan jama'a. Waɗannan zanga-zangar da aka shirya, waɗanda suka fara ranar Juma'a 20 ga Nuwamba da taken "Mu yi yaƙi don makomarmu, ba don yaƙe-yaƙensu ba," ana sa ran za su ci gaba cikin ranakun 21 da 22 ga Nuwamba.
-
Washington A Matsayin Mai Bawa Baghdad Umarni; Me Amurka Ke Nema Ga Firaministan Iraki?
Sabuwar buƙatar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta Amurka ga firaministan Iraki kan aiwatar da alkawuransa ga Washington, ta sake tayar da batun tsoma bakin Amurka cikin shawarwari da kudurorin mulkin Baghdad; shin cibiyoyin doka na wannan ƙasar ne ke tantance makomar siyasa da tsaron Iraki ko Fadar White House?!
-
Khalil Al-Hayya: Yaƙi Da Shirin Sahayoniya Ya Zarce Falasɗinu
Hamas: Cimma Burin Abin Da Ake Kira "Babbar Isra'ila," Ya Zarce Matakin Shiri Da Iƙirari Ya Shiga Matakin Aikitawa.
Khalil Al-Hayya, shugaban ofishin siyasa na Hamas, tare da bayyana cewa yaƙi da shirin Sahayoniya bai takaita ga ƙasar Falasɗinu ba, ya ɗauki cewa hare-haren gwamnatin Sahayoniya kan ƙasashen yankin a matsayin alamar faɗaɗa faɗin wannan shiri na babakere.
-
Yunkurin Raya Cibiyoyin Daukar Sojojin Haya A Siriya; Shin Kungiyoyin "Al-Amashat" Da "Al-Hamzat" Za Su Tafi Yemen Ne?
Ganawar ministan tsaron gwamnatin Jolani da tsoffin kwamandojin ƙungiyoyin "Al-Amashat" da "Al-Hamzat" a daidai lokacin da ministan harkokin wajen wannan gwamnatin ya ziyarci Riyadh da Ankara, ya sake ƙara hasashe kan rawar cibiyoyin daukar mayaƙa wajen tura mayaƙan Siriya zuwa Yemen.