-
hidimaSarkin Spain A Majalisar Dinkin Duniya: Dole Ne Gwamnatin Sahayoniya Ta Daina Kashe Mutanen Da Ba Su Ji Ba Ba Su Gani Ba A Gaza
A taron Majalisar Dinkin Duniya, Sarki Felipe na shida na Spain ya yi kakkausar suka kan laifukan da sojojin Isra'ila suke aikatawa a Gaza tare da yin kira da a kawo karshen hare-haren da ba…
Sabbin labarai
-
hidimaSarkin Spain A Majalisar Dinkin Duniya: Dole Ne Gwamnatin Sahayoniya Ta Daina Kashe Mutanen Da Ba Su Ji Ba Ba Su Gani Ba A Gaza
A taron Majalisar Dinkin Duniya, Sarki Felipe na shida na Spain ya yi kakkausar suka kan laifukan da sojojin Isra'ila suke aikatawa a Gaza tare da yin kira da a kawo karshen hare-haren da ba su dace ba a kan fararen hula. A cikin jawabin nasa, ya jaddada cewa kasashen duniya ba za su iya yin shiru a kan kisan kananan yara da mata na Palasdinawa ba, kuma mafita daya tilo ita ce kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
-
hidimaSanarwar Sojojin Yaman Kan Harin Jiragen Sama A Eilat Da Beersheba
Kakakin Rundunar Sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya sanar a yau Laraba da dare cewa: Rundunar sojin Yaman ta kai wani farmaki mai inganci da jirage marasa matuka a kan wasu wurare biyu na makiya Isra'ila a yankin Umm al-Rishrash da ke kudancin Falasdinu aka mamaye.
-
hidimaShugaba Pezeshkian: Iran Ta Sha Tabbatarwa, Tare Da Babbar Azama Madawwamiya,Cewa Ba Za Ta Durkusa A Gaban ‘Yan Mamaya Ba.
Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Masoud Pezeshkian ya ce: Iran a matsayinta na kasar da ta fi dadewa a ci gaba da wayewa a duniya, ta yi tsayin daka kan guguwowi a tsawon tarihi, wannan al'umma ta sha tabbatar da cewa ba za ta durkusa a gaban mamaya ba, a yau kuma ta tsaya tsayin daka wajen tinkarar mamaya, tana mai dogaro da karfin imani da hadin kan kasa.
-
hidimaMutane 95 Ne Suka Yi Shahada A Gaza, Ciki Mutane 11 Sun Yi Shahada A Layin Karbar Agaji
Tun daga safiyar yau Laraba zuwa yanzu mutane 95 ne suka yi shahada a Zirin Gaza, wadanda akasarinsu an rubuta su ne a birnin Gaza.
-
hidimaJagora: Duk Tattaunawar Da Amurka Ke Kayyade Sakamakonta Tun Farko Ba Ta Da Wani Amfani Kuma Mai Cutarwa Ce Ga Al’umma
A cikin jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi ga al'ummar kasar ta gidan talabijin a daren jiya ya bayyana ci gaba da hadin kai da amincin al'ummar Iran a matsayin dunkulallun karfen kafa na yaki da rarrabuwar kawunan da makiya suke buri ya faru a Iran. Ya bayyana dalilin da ya sa al'ummar Iran masu kishin kasa ba su mika wuya ga matsin lamba da barazanar da makiya suke yi na yin watsi da fasaha mai cik da amfani na inganta sinadarin Uranium ba, ya kuma jaddada cewa: Duk Tattaunawar da Amurka ke kayyade sakamakonta tun farko ba ta da wani amfani kuma mai cutarwa ce ga Al’umma, domin tana sanya makiya azzalumai kwadayin dora wata manufar siyasa ta gaba, kuma ba za ta hana wata cutarwa a gare mu ba, kuma irin wannan tattaunawar babu wata al’umma madaukakiya ma’abuciyar siyasa da hankali d azata amince da ita.
-
hidimaJirgin Saman Yaman Ya Kai Hari Tashar Jiragen Ruwa Na Eilat + Bidiyoyi
A cewar majiyoyin labarai, an tabbatar da cewa yahudawan sahyuniya 4 ne suka jikkata sakamakon wani hari da wani jirgin yakin Yaman mara matuki ya kai a tashar jiragen ruwa ta Eilat kaitsaye.
-
hidimaMa'ajiyar Bama-Bamai Ta Fashe A Pakistan Mutane 24 Sun Mutu
Kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa 'yan sandan sun danganta fashewar wata ma'ajiyar bama-bamai na kungiyar 'yan ta'adda ta "Tehreek-e-Taliban Pakistan", amma wasu mazauna yankin sun tabbatar da cewa harin da sojoji suka kai shi ne ya haddasa shi.
-
hidimaLabarai Cikin Hotuna | Yadda Falasdinawa Ke Yin Hijra Daga Gaza
Labarai Cikin Hotuna | Yadda Falasdinawa Ke Yin Hijra Daga Gaza
-
hidimaRahoto Cikin Hotuna | Bukin Makon Difa’u Muqaddas a Haramin Sayyida Ma’asumah (AS)
Rahoto Cikin Hotuna | Bukin Makon Difa’u Muqaddas a Haramin Sayyida Ma’asumah (AS)
-
hidimaBen-Guer: Idan Da Ni Ne Firayim Minista, Da Na Kama Mahmoud Abbas Nan Take
Ministan tsaron cikin gida na Isra'ila ya sanar da cewa idan shi ne firaministan kasar nan take zai kama Mahmud Abbas shugaban hukumar Falasdinu.