27 Satumba 2026 - 21:07
Source: ABNA24
Iran: Ta Sake Kame Wani Jirgin Ruwan Ƙarƙashin Ruwa Na Amurka Karo Biyu A Mashigar Hormuz

zuwa yanzu Iran ta kama jirage ruwa na ƙarƙashin ruwa na zamani guda biyu marasa matuƙi daya kirar (Automatic Underwater Vehicle [AUV]) na biyu kuma kirar "Dive-LD".

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Mujahidai na sojin ruwa na Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci, da taimakon Allah Maɗaukaki, a cikin wani aiki sun kama jirgin ruwa na ƙarƙashin ruwa na zamani na biyu maras matuƙi (Automatic Underwater Vehicle [AUV]) na sojojin ta'addancin Amurka, wanda ke aiki wajin leƙen asiri a mashigar Hormuz.

Ya kamata a tuna cewa a baya ma, sojin ruwa na Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci — kwanan nan — a wani aiki a ƙofar shiga mashigar Hormuz a tsanake sun kama wani jirgin ruwa na ƙarƙashin ruwa na Amurka maras matuƙi "Dive-LD".

…………..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha