Kamfanin dillancin labaran Ahlulbayt na kasa da kasa (ABNA) ya bayar da rahoton cewa, shugaba Pezeshkian ya jaddada a cikin jawabinsa na taron shekara shekara na majalisar dinkin duniya karo na 80 a yua Laraba cewa "Al'ummar Iran a lokacin da suka kare kansu cikin jaruntaka na tsawon kwanaki goma sha biyu sun nuna wa masu wuce gona da iri cewa lissafinsu ba daidai ba ne". Ya kara da cewa "makiya Iran ba da gangan ba sun ba da gudummawa wajen karfafa hadin kan kasa mai tsarki a cikin kasar".
Shugaban ya kara da cewa: Al'ummar Iran duk da takunkumin karya tattalin arziki mafi tsayi da dadewa da aka yi musu, da yakin kafofin watsa labarai da yakin tunani, da yunkurin haddasa fitina, sun tsaya tsayin daka da tun farkon saukar harsashi na farko a kasarsu, sun tsaya tsayin daka a kan hadin kan da goyon bayan sojojinsu.
Ya yi nuni da cewa, taken Majalisar Dinkin Duniya na bana shine: “Shekaru Tamanin da Karin Zaman Lafiya, Ci Gaba, da ‘Yancin Dan Adam,” cewa wannan taken yana dauke da kira zuwa ga tallafawa ga hadin kai da kuma hangen nesa iri daya don samun kyakkyawar makoma. Haka nan kuma ya jaddada cewa: Akidar addini ta al'ummar Iran da koyarwar dukkan annabawa (amincin Allah ya tabbata a gare su) sun ginu ne a kan tsarin daidaito a tsakanin bil'adama, kuma abin da ke kara daukaka mutum shi ne takawa bisa tsarin gaskiya, hankali, tsarkin zuciya, da son sauran mutane.
Pezeshkian ya bayyana cewa ƙa’idar da ke cewa: “Kada ka yi wa wasu abin da ba ka so wa kanka” ta samo asali ne daga dukan addinan Allah da lamiri na ɗan adam. Ya kawo maganar Annabi Isa Almasihu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa: “Ku yi mu’amala da mutane kamar yadda kuke so su yi muku,” da kuma hadisin Annabi Muhammad (SAW) cewa: “Dayanku ba zai yi imanai ba har sai ya sowa dan uwansa abun da ya sowa kansa”. kuma kamar yadda mai hikima Hillel ya ce a cikin Attaura, "Abin da kuke ƙiwa kanku, kada ku yi wa wasu". Ya yi nuni da cewa "al'adun Gabas da falsafar kyawawan dabi'u duk sun zo kan hakikar gaskiya daya".
Shugaban kasar ya ci gaba da tambaya cewa: Shin duniyarmu a yau tana kan wannan ka'ida? Ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata an fuskanci kisan gilla a Gaza, ana ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon, da lalata kayayyakin more rayuwa a Syria, da kai hari kan al'ummar Yemen, da yunwatar da kananan yara a hannun iyayensu, da kai hare-hare kan ikon mallakar kasashe, da kuma kai hari kan shugabannin al'ummomi, dukkansu tare da cikakken goyon bayan manyan kasashen duniya da masu mafi yawan makamai a karkashin gwamnatocin duniya bisa fakewa da kariyar kai.
Ya ci gaba da cewa: "Shin kun yarda da wadannan laifuffukan da kanku? Wane ne ainihin barazana ga zaman lafiyar yankin da ma duniya baki daya? Wanene ke barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa? Wanene ke keta ka'ida ta zinare ta dabi'ar dan Adam?"
Your Comment