14 Satumba 2025 - 09:19
Source: ABNA24
Shaikh Zakzaky H: Hadin Kai Umarni Ne Daga Allah, Ku Yi Riko Da Igiyar Allah, Kada Ku Rarraba".

Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) Allamah Shekh Ibrahim Zakzaky H ne ya gabatar da jawabin rufe taron makon hadin kai a Abuja ranar Laraba Ina a jawabinsa ya yi gargadi akan hare-haren da ake kaiwa kasashen musulunci, tare yin kiran hadin kai.

Kamfanin Dillancin Labarai na AhlulBaiti (A.S.): A cewar shafin yanar gizon IMN, jagoran ya yi jawabi ta yanar gizo a lokacin da yake Iran. Ya taya al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen al'umma, fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka.

Da yake bayyana watan da aka haifi Manzon Allah (saww) a matsayin lokaci na hadin kan al'ummah, ya ce: "Makiya ba su boye kiyayyarsu ga musulmi ba, sun fito fili sun bayyana cewa ba su da makiyi face musulmi. Makiya Musulunci sun ci gaba da yunkurinsu na rusa kasashen musulmi, kamar Libya da suka yi nasarar ruguzawa, da kuma Sudan da ke fama da rikici a halin yanzu, sun kuma lalata kasashen Siriya, Afganistan da Iraki.

Jagoran ya kara da cewa: "Wannan lokaci ne da ya dace da Musulmi su hada kansu da kansu, ba tare da barin makiya Musulunci su tunzura mu a kan junanmu ba, hadin kai umarni ne daga Allah, ku yi riko da igiyar Allah, kada ku rarraba". Ya kuma jaddada cewa rarrabuwar kai haramun ce a Musulunci saboda munanan sakamakonsa.

A yayin gabatar da jawabai na kwanaki biyar, malamai daga mazhabobi daban-daban sun gabatar da jawabai kan batutuwan da suka shafi hadin kan al'ummar musulmi.

Your Comment

You are replying to: .
captcha