22 Mayu 2025 - 22:37
Source: ABNA24
Bidiyon Mummunan Tarko Da Qassam Suka Wa Sojojin Isra'ila A Jabaliya

Dakarun Qassam sun kai farmaki a gabashin sansanin Jabalia kan sojojin Isra'ila tare da yi masu mummunar barna.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa: Dakarun Al-Qassam reshen soja na Hamas sun fitar da bidiyon wani harin kwantan bauna da wasu dakarunta suka wa sojin Isra'ila da suke cikin motocin yaki a ranar 03/12/2024 a gabashin sansanin Jabalia da ke zirin Gaza.

Rundunar ta Al-Qassam ta sanar da cewa yanayin tsaro ne ya janyo tsaikon fitar da bidiyon wannan aikin na soja.

Your Comment

You are replying to: .
captcha