31 Yuli 2025 - 17:17
Source: ABNA24
Tawagogin Musulmai Sun Nuna Adawarsu Ga Halartar Kakakin Majalisar Knesset A Taron Geneva + Bidiyo

Tawagogin ƙasashen Musulmi sun yi zanga-zangar adawa da halartar Kakakin Majalisar Knesset a taron Geneva + Bidiyo

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Wasu tawagogin Larabawa da ke halartar taron shugabannin majalisar dokokin duniya karo na 6 a birnin Geneva sun bar zauren taron mintuna kadan kafin jawabin shugaban majalisar Knesset na Isra'ila.

Kafofin yada labaran kasar Isra’ila sun wallafa wasu bidiyo da ke nuna cewa wasu tawagogin kasashen larabawa da suka hada da wakilan Iran da Falasdinu da kuma Yemen sun fice daga taron shugabannin majalisar dokokin duniya kafin jawabin Amir Ohana, shugaban majalisar Knesset na Isra’ila.

A ranar Talata ne aka fara taron shugabannin majalisar dokokin duniya karo na 6 a birnin Geneva na kasar Switzerland. Manufar wannan taro ita ce karfafa hadin gwiwa da tattaunawa tsakanin majalisun dokokin kasashen duniya.

Ohana ya yi kalamai masu tayar da hankali a cikin jawabinsa, inda ya ce: "Shin kuna son kasar Falasdinu ne? Ku kafa ta a London ko Paris, domin titunan da ke wurin a yanzu sun yi kama da Gabas ta Tsakiya".

Your Comment

You are replying to: .
captcha