19 Satumba 2025 - 15:34
Source: ABNA24
Yaman: Man Fetur Ɗin Ƙasashen Larabawa Ne Isra'ila Ke Anfani Da Shi Wajen Jefa Bama-Bamai Kan Al'ummar Gaza.

Sayyid Abdul Malik Badreddin Al-Houthi ya ce: Makiya yahudawan sahyoniya suna amfani da bama-bamai na Amurka, Birtaniya da Jamus, wadanda man fetur din kasashen Larabawa ke samar musu da man fetur, wajen aiwatar da kisan kiyashi a Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdul Malik Badreddin Al-Houthi ya bayyana a yammacin jiya Alhamis a jawabinsa dangane da laifukan da yahudawan sahyoniya suke aikatawa a Gaza da kuma sabbin abubuwan da suke faruwa a yankin da ma duniya baki daya: Makiya yahudawan sahyoniya suna ci gaba da aikata laifukan ta'addancin karni a Gaza a gaban idon duniya, kuma ganin wannan adadi na kisan kiyashi da bala'i zai sa duk wanda ya yake da kwayar zarra na tausayi ya tausaya.

Makiya yahudawan sahyoniya suna amfani da bama-bamai na Amurka, Birtaniya da Jamus, wadanda kasashen Larabawa ke samar masu da man fetur ɗin da suke amfani da shi, wajen aikata kisan kiyashi a Gaza.

Makiya haramtacciyar kasar Isra'ila suna cin gajiyar raunin kasashen musulmi wajen aiwatar da mumman hadafinsu. Barazanar da Isra'ila ke yi kan al'ummar musulmi baki daya ce, kuma ba za ta tsaya ga Falasdinu kadai ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha