Kamfanin dillancin labaran Ahlulbayt na kasa da kasa (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: Philip VI ya yi jawabi a taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a ranar Laraba 24 ga Satumba, 2025 (2 Mehr 1404). Ya kuma yi Allah wadai da munanan manufofin siyasar gwamnatin sahyoniyawan a Gaza.
Yayin da yake magana kan harin bama-bamai da aka kai a asibitoci da makarantu da cibiyoyin ‘yan gudun hijira, ya ce: “Wadannan ayyuka ne masu banƙyama da ke cutar da lamirin bil’adama, dole ne al’ummar duniya su yi magana, domin ci gaba da kai hare-haren ba wai kawai ga al’ummar Palasdinu ba ne,har ma yana barazan ga wanzuwar mutuncin dukan bil’adama ne”.
Sarkin Spain ya yi amfani da kalmar “kisan kiyashi” don kwatanta ayyukan Isra’ila, yayin da yawancin gwamnatocin Yammacin Turai har yanzu ba su yi amfani da irin wannan kalmar ba. Ya kuma yi watsi da hujjojin Tel Aviv, yana mai ishara da cewa: "Babu wani uzuri da za’a fake da shi wajen kai harin bam ga mata, yara da 'yan gudun hijira marasa tsaro".
Jawabin nasa ya zo ne a daidai lokacin da Isra'ila ke fuskantar kyama daga kasashen duniya da kuma matsin lamba ga Amurka, babbar aminiyar Tel Aviv, na ta daina dakile kudurorin neman goyon bayan al'ummar Palasdinu.
A karshe ya yi kira ga kasashen duniya da su yi “Jarumtar Halaye,” yana mai kira ga gwamnatoci da su tsaya tare da al’ummar Palastinu da ake zalunta maimakon tallafa wa ‘yan mamaya kuma kada su bari tarihi ya sake shaida kisan kiyashi da share wata al’umma.
Your Comment