4 Maris 2025 - 22:19
Yadda Ruhiyyar Imani Ke Ƙara Ƙarfi Da Azamar Ɗan Adam

Waliyyan Allah na gaskiya kuma ba su da ‘yanci daga kowane irin maɓuɓɓuga suke sun kubuta daga bautar abin duniya, kuma gudun duniya a ma’anarsa na gaskiya shi ke juya su kuma ba sa firgita kokawa dan sun rasa wani abin duniya, haka nan kuma tsoro baya shagaltar da tunaninsu a cikin irin wadannan abubuwa.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya kawo maku bayani dan dangane da muhimmancin Imani a rayuwar dan Adam in da ya fara da bayanin cewa: akwai matsaloli a rayuwar dan adam a ko da yaushe, kuma wannan ita ce dabi’ar rayuwar duniya da ma, kuma gwargwadon girman dan’adam gwagwadon irin girman matsalar da zai hadu da ita kenan, wadannan matsalolin, don haka ne mutum zai iya fahimtar girman matsalolin da Manzon Allah (saww) ya fuskanta a cikin kiransa mai girma.

Amma muka ga cewa Allah ya umurci Annabinsa da ya koma ga yin tasbihi da addu'a da sujada a halararsa domin samun karin karfi da karfin gwiwa wajen fuskantar wadannan dimbin matsalolin da suke fuskanta.

Allah yana cewa a cikin suratul Hijir aya ta 97-99:

وَلَقَدْ نَعْلَمُ أَنَّكَ يَضِيقُ صَدْرُكَ بِمَا يَقُولُونَ (97) فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَكُنْ مِنَ السَّاجِدِينَ (98) وَاعْبُدْ رَبَّكَ حَتَّى يَأْتِيَكَ الْيَقِينُ (99)

"Kuma lalle ne mu, mun sani cewa kana yin bakin ciki a kan abin da suke fada, saboda haka ka yi tasbihi ga Ubangijinka, kuma ka kasance daga masu sujada, kuma ka bauta wa Ubangijinka har mutuwa ta zo maka”.

Haka nan kuma bisa amfani da ruwayoyi daban-daban da suka zo da cewa, a lokacin da manyan shugabanni suka fuskanci rikici da matsaloli masu yawa, su kan tafi ne zuwa ga dakin Allah su samu natsuwa da karfi ta fuskar yin ibadarsa.

A cikin suratu As-Saff, Alkur’ani mai girma ya dauki imani a matsayin babbanjari domin samun ceto da mafuta:

يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَى تِجَارَةٍ تُنْجِيكُمْ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ (10) تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَتُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ بِأَمْوَالِكُمْ وَأَنْفُسِكُمْ ذَلِكُمْ خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُونَ (11)

“Ya ku wadanda kuka yi imani, shin ba na shiryar da ku zuwa ga sana’ar da za ta tserar da ku daga azaba mai radadi? "Ku yi ĩmãni da Allah da Manzonsa, kuma ku yi jihãdi a cikin tafarkin Allah da dũkiyõyinku da rãyukanku. Wanca nan ku shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kuna masu sani".

A cewar wannan ayar, imani babban jari ne kuma amfani da shi yana bukatar fasaha da hikima. Don haka, gwargwadon ƙwarewar mai shi, gwagwargwadon mafi girman yawan anfanuwa da zai yi sa me shi.

A cikin aya ta 29 a cikin suratu Anfal, mun ga cewa imani yana ba wa mutum hangen nesa:

يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ تَتَّقُوا اللَّهَ يَجْعَلْ لَكُمْ فُرْقَانًا وَيُكَفِّرْ عَنْكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ (29)

“Ya ku wadanda kuka yi imani, idan kun bi Allah bisa takawa, zai ba ku hankalta (ta banbance dai-dai da ba dai ba). Kuma Ya kankare muku zunubanku, kuma Ya gãfarta muku Kuma Allah Ma’abucin falala ne mai girma".

Kasancewar taqawa da imani suna sanya mutum ganin haqiqa da kubutar da shi daga fadawa tarkon kura-kurai, hakan ya zo a cikin alqur'ani mai girma ta hanyoyi daban-daban.

Kasancewar muminai da salihai suna da alaka da tushen gaskiya, wani nau’in sanin hakikanin al’amura yana rayuwa a cikin zukatansu, kuma suna kallon al’amura ta wurin Allah, don haka ne ba sa fadawa tarkon bata da kura-kurai na wasu.

Tsoro yawanci yana tasowa ne daga yiwuwar rasa albarkar da mutum yake da shi ko kuma haɗarori da za su iya yi masa barazana a nan gaba, kamar yadda baƙin ciki yakan samo asali ne daga rasa abubuwan da suka gabata da kuma rashin damar da samunsu.

Waliyyan Allah na gaskiya kuma ba su da ‘yanci daga kowane irin maɓuɓɓuga suke sun kubuta daga bautar abin duniya, kuma gudun duniya a ma’anarsa na gaskiya shi ke juya su kuma ba sa firgita kokawa dan sun rasa wani abin duniya, haka nan kuma tsoro baya shagaltar da tunaninsu a cikin irin wadannan abubuwa.

Don haka baqin ciki da fargabar da ke sa wasu su kasance cikin rashin nutsuwa da damuwa game da abin da ya gabata da wanda zai nan gaba ba su da gurbi a rayuwarsu.

Wadannan su ne wadanda suka mallaki wadannan ginshiqan addini da xabi’u guda biyu, suke samun natsuwa a cikin ruhinsu, ta yadda babu wani guguwar rayuwa da ke girgiza su.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam) ya ce: “Tabbatuwar Mumini wajen tabbatar da imaninsa ya fi girma fiye da kafuwar tsaunuka da suke jijiyoyi a cikin kasa, domin Mumini an sassaka shi sama da dutse, amma babu wanda yake da ikon tauye addinin mumini koda kadan ne.”

Muhimmancin Imani Da Girman Mumini

Ruwayoyin sun qunshi bayanin martaba da muhimmancin imani da kuma girmama mumini, wanda a ganin hakan mutum kawai sai dai ya yi mamakinsu. Daga ciki akwai:

A. Imam Sadik (AS): "Alfarmar mumini ta fi alfarmar Ka'aba".

B. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Na rantse da daukakata da girmana! "Ban halicci wani wanda yafi soyuwa a gareni sama da bawa mumini...".

Akwai ayoyi a cikin Alkur'ani mai girma da suka bayyana adadin bayi na gaskiya da cewa su yan kadan ne. "Daga cikin bãyina kaɗan ne masu gõdiya,"

يَعْمَلُونَ لَهُ مَا يَشَاءُ مِنْ مَحَارِيبَ وَتَمَاثِيلَ وَجِفَانٍ كَالْجَوَابِ وَقُدُورٍ رَاسِيَاتٍ اعْمَلُوا آلَ دَاوُودَ شُكْرًا وَقَلِيلٌ مِنْ عِبَادِيَ الشَّكُورُ (13)

"Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Nũhu ba su kasance ba fãce kaɗan".

حَتَّى إِذَا جَاءَ أَمْرُنَا وَفَارَ التَّنُّورُ قُلْنَا احْمِلْ فِيهَا مِنْ كُلٍّ زَوْجَيْنِ اثْنَيْنِ وَأَهْلَكَ إِلَّا مَنْ سَبَقَ عَلَيْهِ الْقَوْلُ وَمَنْ آمَنَ وَمَا آمَنَ مَعَهُ إِلَّا قَلِيلٌ (40)

An yi bayani adadin muminai yan kadan ya zo a cikin wadannan hadisai, don haka darajar imani da girmansa ba a boye ta ke ba. Idan har imani shine darajar duniya da lahira; Idan har mumini ya kasance mafi soyuwar halittun Allah a bayan kasa; Kuma idan har mumini ya fi Ka'aba alfarma, to imani da girman mumini da kaskancin kafiri ba su da iyaka kenan.

Imani shi ne hanyar da mutum zai samu tsaro ta hanyarsa, domin imani shi ne aminci na asali, kuma jikin mutum da ruhinsa suna rayuwa ne kawai ta hanyar imani kuma su zama masu girma da daraja a wurin Allah.

Imam Ali (AS) yana cewa: "Mutum ba ya dandana gaskiyar imani face ya kasance yana da siffofi guda uku: fahimtar addini, da hakuri a cikin musibu, da kyakkyawan hukunci da lura a cikin sha'anin rayuwa".

Imani ya zo da siffofi guda uku: na farko, fahimta a cikin al’amuran addini; Wato mumini ya san al'amuran addini da na akida da a aikace, kuma yana da hazaka wajen sanin al'amuran da suke faruwa a cikin rayuwarsa ta daidaiku ko ta gamayya da amfani da su a cikin lamurran addininsa.

Na biyu, ya kasance mai haƙuri a cikin wahala da musibu. Wato yana ganin bala'i da wahalhalu na rayuwa suna da manufa. Matsalolin ko dai na cikar halittar mutum ne ko don rage nauyin zunubi.

Na uku, mumini yana da hankali kuma yana da tsare-tsare da tsantseni a rayuwarsa da al'amuransa na yau da kullun. Ba wai ya kamu da son rayuwar yau da kullun ba kuma yana son duk abin da ya zo masa.

Kamar yadda wannan hadisin yake nuni da cewa, mumini ba wai yana da kaddara da tsari kadai ba, har ma yana da kyakkyawar makoma da hangen nesa.

Abin sha'awa a cikin wannan hadisi shi ne tafsirin dandanon imani, wanda ke nuni da cewa imani ana iya dandana shi kuma a same shi, kuma yana da dandano mai dadi ta yadda duk wanda ya dandana shi ya zama cikin mararinsa, kuma ya tabbatu akan ma'auni mai dadi na imani da dadin dandanonsa.

Tabbas imani ba busasshiyar akida ba ne ko kuma kawai maganar a baki, a'a ruhi ne da ake hura a cikin jikin kafirai marasa rai kuma yana shafar dukkan halittunsu, ya zamo kunnuwansu kuma suna da karfin ji, harshensu kuma ikon magana ne, hannayensu da kafafunsu kuma suna da ikon yin kowane aiki mai kyau.

Bangaskiya Imani yana canza daidaikun mutane, tana shafar su a tsawon rayuwarsu, kuma tana bayyana tasirin rayuwa ta kowane fanni.

Allah yana cewa a cikin suratun An'am:

أَوَمَنْ كَانَ مَيْتًا فَأَحْيَيْنَاهُ وَجَعَلْنَا لَهُ نُورًا يَمْشِي بِهِ فِي النَّاسِ كَمَنْ مَثَلُهُ فِي الظُّلُمَاتِ لَيْسَ بِخَارِجٍ مِنْهَا كَذَلِكَ زُيِّنَ لِلْكَافِرِينَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (122)

"Shin, wanda ya kasance matacce sa'an nan Muka rãyar da shi, kuma Muka sanya masa wani haske da yake iya tafiya da shi a cikin mutane, zai zamo kamar wanda yake a cikin duffai, wanda bã ya iya fita daga gare shi?" Kamar wanca nan ka ne ayyukan da suka kasance suna aikatawa aka kawata su ga kafirai.

Ko da yake dole ne a sami bangaskiya ta hanyar ƙoƙari na mutum da kansa, waɗannan ƙoƙarin ba zai kai ko'ina ba sai idan har ba ai kokarinsa daga Allah ba ina zai je. Sannan Ya ce: Mun sanya wa irin wadannan mutane wani haske da za su yi tafiya da shi a cikin mutane.

Duk da cewa malaman tafsiri sun bayar da fassara daban-daban dangane da ma'anar wannan haske, amma da alama ba wai kawai yana nufin Alqur'ani da koyarwar Manzon Allah (SAW) ba ne, bugu da kari imani da Allah yana ba mutum sabon haske da fahimta, yana ba shi haske na musamman, ya kuma fadada hangen nesansa fiye da takaitaccen rayuwar abin duniya da iyakokin duniya guda hudu, yana nutsar da shi cikin wani yanayi mai tsananin gaske.

Kuma saboda yana kiransa zuwa ga kyautata gina kansa, yana cire mayafin son kai, da ganin kai, son zuciya, son ra, taurin kai, da shashanci a gaban idanun ruhinsa, yana ganin gaskiyar da bai taba iya fahimtarta a baya ba.

Ta fuskar wannan haske yana iya samun hanyarsa ta rayuwa a tsakanin mutane, kuma a kiyaye shi da kiyaye shi daga yawancin kura-kurai da wasu ke faxawa a cikin su saboda kwadayi, ta dalilin yin kuntataccen tunani bin duniya, ko rinjayar son zuciya da son rai.

Magora:

1- Alqur'ani mai girma

2- Morteza Motahari, Insan Wa Iman

3- Morteza Motahari, Bisti Guftar

4- Morteza Motahari, Ashnayi wa qur’ani Juzu’i na 4

5- Nasser Makarem Shirazi, Tafsiri Namune, Juzu'i na 7

6- Mujallar Pegah Hawza

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha