5 Satumba 2025 - 14:03
Source: ABNA24
Bidiyon Yadda Jiragen Ruwan Ƙasashen Turai Ke Tafiya Zuwa Gaza

Kungiyar Al-Samoud Global Flotilla ta sanar da cewa Hukumar Agajin Gaggawa ta Italiya ta aika jirgin ceton ta, Life Sport, don shiga cikin jerin jiragen ruwa da ke kan hanyarsu ta zuwa Gaza domin kai ɗauki.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Jirgin ruwan zai hade da jiragen ruwa da dama da suke dauke da daruruwan mutane daga kasashe daban-daban har 44 domin karfafa agajin da ake yi a Gaza, kamar yadda tashar jiragen ruwa ta Al-Samoud Flotilla ta tabbatar.

Jirgin mai tsawon mita 51, wanda ya saba gudanar da ayyukan ceto bakin haure a tekun Mediterrenean, a wannan karon zai ba da tallafin magunguna da kayan aiki ga mutanen Gaza.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha