Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: An fara taron kasa da kasa kan hadin kan musulmi karo na 39 a yau Litinin 8 ga watan Satumba, 2025 a dakin taro na kasa da kasa tare da halartar shugaban kasar Masoud Pezzekian da gungun malamai daga kasashen musulmi fiye da baƙi 80 na duniya da baƙi na cikin gida 210 ne ke halartar taron. Har ila yau, an karɓi takardu 148 daga cikin 392 da aka ƙaddamar don gabatarwa a taron. Za a gudanar da wannan taro na tsawon kwanaki 3 daga ranar 8 zuwa 10 ga watan Satumba a karkashin kulawar Majalisar Kusanto da Mabiya Addinin Musulunci, taron mai taken "Annabin Rahma da Al’umma Daya".

8 Satumba 2025 - 15:01
Source: ABNA24

Your Comment

You are replying to: .
captcha