Afganistan
-
Afganistan: Al'ummar Ghor Sun Taimaka Wa Al’ummar Gaza Da Afghani 454,000
Jami'an yankin lardin Ghor sun bayyana cewa bayan gudanar da wani yaƙin neman taimako na jama'a, an tattara taimakon kuɗi na Afghani 454,000 don tallafawa iyalan da hare-hare suka shafa a Gaza kuma an aika zuwa wannan yankin.
-
Afganistan: Taliban Sun Rufe Asibitin Fatimah Al-Zahra (A.S) A Yammacin Kabul
Sojojin ma'aikatar shari'a ta Taliban a yau sun rufe asibitin Fatimah Al-Zahra (A.S) a Kabul wanda aka gina da goyon bayan Iran; matakin da ke ci gaba da jerin matakan da wannan ma'aikatar ta ɗauka na rufe cibiyoyin addini, ilimi da al'adu masu alaƙa da Shi'a na Afghanistan cikin watannin da suka gabata.
-
Majalisar Ƙoli Ta Gwagwarmayar Ƙasa Don Ceton Afghanistan Tayi Allah-Wadai Da Manufofin Taliban
Rufe Jami'ar Khatam Al-Nabiyyin (S.A.W) Shaida Ce Ga Ƙiyayyar Da Taliban Ke Yi Ga Ilimi
Gwagwarmayar Ƙasa Don Ceton Afghanistan ta fitar da wata sanarwar Allah-wadai da tsanantar manufofin danniya, nuna bambanci, keɓewa da keta haƙƙoƙin asali na al'ummar ƙasar da ƙungiyar Taliban ke yi kuma a wani ɓangare nata ta ɗauki rufe Jami'ar Khatam al-Nabiyyin (S.A.W) a matsayin shaida ta ƙiyayyar Taliban ga ilimi.
-
Ƙoƙarin Taliban Na Daidaita Dangantaka Da Washington
Afghanistan Da Amurka: Muttaqi Da Khalilzad Sun Tattauna Game Da Fadada Dangantakar Juna
Amir Khan Muttaqi, ministan harkokin wajen Taliban, ya gana da Zalmay Khalilzad, tsohon wakilin musamman na Amurka a harkokin Afghanistan, a Kabul, inda suka tattauna game da fadada dangantaka da Washington, damar zuba jari, da "mu'amala mai ma'ana" tsakanin bangarorin biyu.
-
Taliban Sun Kewaye Makarantar Hauza Ta Khatamul-Nabiyyin Sun Bukaci Kowa Ya Fice
Sojojin Taliban a yau Asabar, 5 ga Satumba, sun kewaye makarantar addini ta Khatamal-Nabiyyin (SAW) a Kabul, kuma sun bukaci jami'ai da daliban addini su kwashe kayansu da ficewa daga wannan cibiyar; matakin da ke ci gaba da matsin lamba fiye da watanni biyu kan ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin ilimi da addini na 'yan Shi'a a Afghanistan.
-
Afghanistan: Fashewar Bam A Yankin Da 'Yan Shi'a Ke Rayuwa A Kabul
Wata fashewa sakamakon jefa gurneti ya faru a gidan burodi da ke gaban babban kanti na "Paywand" a Dasht-e-Barchi da ke yammacin Kabul.
-
Afghanistan: An Kashe Sojojin Taliban 6 Da Raunata 8 A Badakhshan
Kungiyar 'Yanci ta Afghanistan ya bayyana cewa dakarunta a rikice-rikicen jiya (Lahadi 16 ga Agusta) a gundumar Zibak na lardin Badakhshan, sun kashe membobin Taliban shida kuma sun raunata wasu takwas, kuma sun sami damar kwace wasu wuraren wannan ƙungiya.
-
Afganistan: Taliban Tana Zartar Da Qudurin Kwace Karamin Birnin Omid-e Sabz Daga Mamallakansa
Jam'iyyar 'Yan Kasa ta Afghanistan ta yi Allah wadai da yunkurin da Taliban ta yanke na korar mazauna garin Omid-e Sabz, kuma ta bayyana shi a matsayin cin zarafin haƙƙin mallaka, tsaron shari'a, da mutuncin dubban iyalai.
-
MDD: Hadarin Fataucin Bil'adama A Afghanistan Ya Na Ƙaruwa
Ofishin yaƙi da muggan ƙwayoyi da laifuka na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa komawar 'yan gudun hijira sama da miliyan shida, rashin aikin yi, talauci, bin bashin iyalai, da rashin hanyoyin rayuwa na dabam, sun sanya 'yan ƙasar Afghanistan su fuskanci fataucin bil'adama, aikin tilas, da sauran nau'o'in cin zarafi fiye da da.
-
UNOCHA: Karancin Kasafin Kuɗi Yana Barazana Ga Ayyukan Ciwarwa Ga Yara Da Mata Miliyan 5.7 A Afganistan
Ofishin Gudanar da Taimakon Bil'adama na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargadin cewa, karancin albarkatun kuɗi ya sanya samun damar yara da mata miliyan 5.7 a Afganistan ga ayyukan lafiya da abinci na yau da kullun cikin hadari mai tsanani.
-
Rikicin Iyaka Tsakanin Afganistan Da Pakistan Na Ci Gaba Tsananta
Majiyoyin Pakistan sun ba da rahoton faruwar rikici tsakanin sojojin Taliban da masu tsaron iyaka na Pakistan a yankunan iyaka na lardin Paktia na Afganistan da Kuram a jihar Khyber Pakhtunkhwa. Wannan rikici ya fara ne bayan harbin da aka yi a kan sansanonin iyaka na Pakistan, kuma sojojin Pakistan a martani sun kai hari a kan wuraren Taliban da manyan bindigogi.
-
Switzerland Ta Ware Dala Miliyan 2.4 Don Tallafawa Shirye-shiryen Jin Kai A Afganistan
Ofishin Hukumar 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) ta sanar da cewa gwamnati da al'ummar Switzerland sun ware dala miliyan 2.4 don ƙarfafa shirye-shiryen jin kai a Afganistan; kasafin kuɗin da aka shirya don tallafawa masu komawa gida, iyalai masu rauni, da al'ummomin da ke karbar bakuncin a yankuna daban-daban na Afganistan.
-
Afganistan: Jirgin Kasa Na Farko Kai Tsaye Daga China Ta Hanyar Iran Ya Isa Herat
Iran Chaina Da Afganistan Na Kara Samar Da Hanyoyin Kasuwanci Ta Kasa
Jirgin kasa na farko na sufuri kai tsaye daga China zuwa Iran da Afganistan, ta hanyar wucewa ta hanyar jirgin kasa na Iran da hanyar Khaf-Herat, ya isa tashar Rozank a lardin Herat; wani lamari da zai iya zama juyi mai muhimmanci wajen hada Afganistan da ke kewaye da ƙasa zuwa hanyoyin kasuwancin yanki, da kuma rage dogaron wannan ƙasa ga hanyoyin gargajiya na Pakistan.
-
Iran: Ta Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Sufuri Tsakaninta Da Afganistan Da Tajikistan
An gudanar da taron bangarori uku na manyan jami'an kasashen Iran, Afganistan da Tajikistan a Mashhad, kuma a ƙarshe, bangarorin sun sanya hannu kan yarjejeniya don bude hanyar sufuri ta manyan motocin daukar kaya ta hadin gwiwa.
-
Labarai Cikin Hotuna | Na Halartar 'Yan Afganistan A Mashhad A Wajen Jana'izar Shahidin Jagora
Baƙi 'yan Afganistan da ke zaune a Mashhad da sauran wadanda suka shigo kasar Iran domin jana’izar Shahidin Jagora, tare da dinbin halartarsu a jana'izar Shahidin Jagoran juyin juya hali da kuma kafa tantinan hidima a wannan taron tarihi, sun sake yin shela da babbar murya game da soyayyarsu ga jagora masoyi na juyin juya hali, amincinsu ga Jamhuriyar Musulunci, da kuma hadin kai da al'ummar Iran, suna masu tabbatar da hakan a aikace. ............
-
Halartar Dinbin 'Yan Afganistan A Jana'izar Shahidin Jagora A Qom + Hotuna
Halartar Dinbin 'Yan Afganistan A Jana'izar Shahidin Jagora A Qom + Hotuna