-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Tarukan Muharram Da Ashura Suna Ci Gaba Da Gudana A Cibiyar Musulunci Ta S.D.O Tanzania
Rahoto Cikin Hotuna | Na Tarukan Muharram Da Ashura Suna Ci Gaba Da Gudana A Cibiyar Musulunci Ta S.D.O Tanzania
-
Ayarin Motocin "Gwagwarmayar Maghrib" Sun Isa Masaukin Farko A Libya + Hotuna
Ayarin motocin sun kunshi masu fafutuka sama da dubu da motocin safa 12 da kuma kananan motoci kusan 100. Bayan wuce garuruwa daban-daban a Tunisiya, ayarin motocin gwagwarmayar Maghreb za su isa Zirin Gaza ta hanyar Libiya da Masar.
-
Labarai Cikin Hotuna | Ayatullah Ramezani Ya Halarci Cbiyar Al'adun Sayyida Zahra (AS) A Abidjan.
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti ta duniya da ya ziyarci wannan kasa ta yammacin Afirka bisa gayyatar malaman addini daga kasar Ivory Coast, ya halarci cibiyar al'adu ta Sayyid Zahra (AS) da ke birnin Abidjan. An gina wannan katafaren ginin ne a shekarun da suka gabata tare da kokarin kungiyar Al-Ghadir na kasar Ivory Coast a wannan birni.
-
Labarai Cikin Hotuna | Ayatullah Ramezani Ya Gana Da Babban Limamin Cocin Katolika Na Ivory Coast
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti ta duniya, wanda ya kai ziyara kasar Ivory Coast bisa gayyatar da malaman addini suka yi masa, ya gana da babban limamin cocin Katolika na kasar Cote d’Ivoire kuma wakilin fadar Vatican Cardinal Ignace Dogbo Bessie.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Taron "Ahlul Baiti (AS), Adalci Da Mutuncin Dan Adam" A Babbar Kasa Ta Ivory Coast
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: an gudanar da taro mai taken Ahlul Baiti (AS), adalci da martabar dan Adam tare da halartar Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya, a jami'ar Al-Mustafa da ke birnin Abidjan na kasar Ivory Coast. Ayatullah Ramezani ya yi tattaki zuwa wannan kasa da ke yammacin Afirka bisa gayyatar malaman addini daga Ivory Coast.
-
Bidiyon Yadda Aka Buɗe Kamfanin Labaran ÀBNA A Nahiyar Afirka Ghana
Bidiyon Yadda Aka Buɗe Kamfanin Labaran ÀBNA A Nahiyar Afirka Ghana
-
Bidiyon Yadda Mabiya Ahlulbaiti AS Suka Gudanar Da Sallar Idi A Ghana
Bayan kammala sallar Idi, Sheikh Bansi ya gabatar da hudubar Idi da harshen Hausa, inda ya mayar da hankali kan halin da al’ummar Falasɗinu ke ciki a halin yanzu.
-
Yadda Mabiya Ahlulbaiti AS Sukai Sallar Idi A Ghana + Hotuna
Yadda Khalifan Shugaban Mabiya Ahlulbait A Ghana, Sheikh Ibraheem Bansi, Ya Jagoranci Sallar Idi a Masallacin Ahlulbayt da ke Madina, Accra
-
An Bude Ofishin Yada Labaran ABNA A Ghana / ABNA Ta Zama Muryar Ahlul Baiti (AS) a Yammacin Afirka
An bude ofishin ABNA a nahiyar Afrika a babban birnin kasar Ghana a wani biki da ya samu halartar babban sakataren majalissar Ahlul Baiti (AS) ta duniya.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Taron "Ahlul Baiti (AS), Adalci da Mutuncin Dan Adam" a Babban Birnin Ƙasar Ghana
Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlulbaiti AS - ABNA - ya kayi rahoton cewa: an gudanar da taro mai taken “Ahlul Baiti (AS) da adalci da mutuncin dan Adam” tare da halartar babban sakataren majalisar Ahlulbaiti AS ta duniya Ayatullah Reza Ramezani a birnin Accra babban birnin kasar Ghana. Ayatullah Ramezani ya yi tattaki zuwa wannan kasa ta yammacin Afirka bisa gayyatar da malaman addini daga Ghana suka yi masa.
-
Labarai Cikin Hotuna | Na Bude Ofishin Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA A Ghana
Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlulbaiti AS - ABNA - ya habarta cewa: an bude ofishin kamfanin dillancin labarai na ABNA a kasar Ghana tare da halartar babban sakataren Majalisar Ahlulbaiti AS ta duniya Ayatullah Reza Ramezani da kuma Hassan Sadraei Aref babban Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA. Ayatullah Ramezani ya yi tattaki zuwa wannan kasa ta yammacin Afirka tare da wata tawaga bisa gayyatar malaman addini daga Ghana.
-
Sheikh Ibrahim Alzakzaky {H}: Allah Ta'ala Yayi Imam Khumaini (QS) Mutum Wanda Ke Da Natsuwa Da Rashin Tsoro
A ranar Talata 3/6/2025 (6/12/1446) ne Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabi ga dalibai da malaman manyan makarantu da ke karkashin inuwar ‘Academic Forum’, a munasabar tunawa da shekara 36 da wafatin Imam Khumaini (QS), a gidansa da ke Abuja.
-
Sheikh Omar Jain Senegal: Iran Tana Cikin Ruhinmu Da Dabi'unmu.
Babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (AS) ta duniya a yayin da yake halartar shelkwatar kungiyar malaman kasar Senegal, ya jaddada wajabcin hadin kan musulmi da karfafa karfin ilimi da addini na duniyar musulmi.
-
Hotuna: Taron "Gudunwar Malaman Musulunci A Ci Gaban Duniya Tare Da Mai Da Hankali Kan Falasdinu" A Senegal
Hotuna: Taron "Gudunwar Malaman Musulunci A Ci Gaban Duniya Tare Da Mai Da Hankali Kan Falasdinu" Da Aka Gudanar A Babban Birnin Kasar Senegal.
-
Yadda Ahlulbayt (AS) Suka Kasance Wajen Adalci Da Mutuncin Dan Adam
Hotuna: Taron Kimiyya Mai Taken "Ahlulbayt (AS) Da Adalci Da Mutuncin Dan Adam" Da Aka Gudanar A Dakar, Senegal
Kamfanin dillancin labaran Ahlulbaiti: An gudanar da taron ilimi na "AhlulBait (a.s.) da adalci da mutuncin dan 'adama" tare da halartar Ayatullah Reza Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (a.s.) ta duniya a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal. Ayatullah Ramazani ya yi tafiya zuwa kasar da ke yammacin Afirka bisa gayyatar da malaman addini na kasar Senegal suka yi masa.
-
Najeriya Ta Karbi Bakuncin Taro Kan Gudunmawar Imam Khumaini Da Tasirinsa A Afirka + Bidiyo
A jiya Lahadi ne aka gudanar da wani taro a birnin Kano da ke arewacin Najeriya domin yin nazari kan rayuwa da kuma gudunmawar marigayin wanda ya kafa jamhuriyar Musulunci ta Iran Imam Khumaini. Kungiyar Zahra ta Najeriya, tare da hadin gwiwar jami’ar Ilimi ta AlMustafa da ke Kano, da kungiyar Academic Forum na Harkar Musulunci ne suka shirya taron.
-
Firaministan Sudan Kamel Idriss ya rusa majalisar ministocin kasar.
Sudan: Majalisar Ministocin Rikon Kwaryar Kasar Ta Rushe
A cewar rahotonnin safiyar yau Litinin daga kanfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) Idriss ya rusa majalisar ministocin kasar domin share fagen kafa sabuwar hukuma da majalisar ministoci.
-
Ayatullah Ramezani A Dakar: Koyarwar Ahlul Baiti (AS) Ita Ce Hanyar Zuwa Ga Ubangiji
Babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ya bayyana hakan a wajen taron makokin shahadar Imam Jawad (AS) da aka gudanar a babban birnin kasar Senegal cewa: “Yin amfani da koyarwa da maganar Ahlulbaiti (AS) yana taimaka mana wajen kusantar Allah ta hanya ta yin aiki, koyarwar Ahlul Baiti (AS) ta tauhidi ce, bisa dabi’a, kuma bisa ga hankali”.
-
Ayatullah Ramazani Ya Isa Senegal + Hotuna
Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlulbaiti (AS) ya yi tafiya zuwa kasar Senegal bisa gayyatar da malaman addini suka yi masa daga cikin jerin kasashen da zai kai wa ziyara a kasashen Afirka.
-
JMAT Ta Yi Allah Wadai Da Rashin Mutuntawar Da Matasan Kenya Su Ka Yi Ga Shugaban Kasar Tanzaniya.
Da yake zantawa da manema labarai, shugaban JMAT, Sheikh Dr. Alhad Mussa Salum, ya ce irin wadannan kalamai da ayyukan ba na tausasawa ba ne kuma suna barazana ga hadin kai da fahimtar juna tsakanin kasashe makwabta da abokai.
-
Rahoton Hotuna | Bikin Yaye Dalibai A Jami'ar Al-Mustafa Da Ke Kasar Nijar
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya habarta cewa: an gudanar da bikin yaye dalibai a jami'ar Al-Mustafa da ke jamhuriyar Nijar a birnin Yamai fadar mulkin jamhuriyar Nijar, tare da halartar Ayatullah Ridha Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya. Ayatullah Ramazani ya yi tattaki zuwa wannan kasa ta yammacin Afirka bisa gayyatar malaman addini daga Nijar.
-
Hotuna | Na Taron Malaman Tabligi Da Daliban Da Suka Kammala Karatun Addinin Musulunci A Nijar
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya habarta cewa: An gudanar da wani gagarumin taro na malaman addinin Musulunci da daliban da suka kammala karatu a Nijar a birnin Yamai, wanda ya samu halartar shugabanin kungiyoyin Musulunci na Nijar da Qutb Tijjaniyya na Nijar. Babban bako na musamman a taron shi ne Ayatollah Reza Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (a.s.) na duniya.
-
Hatuna | Yadda Ayatullah Ramezani Ya Nada Rawani Ga Gungun Dalibai A Nijar
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya habarta cewa: an gudanar da bikin nada rawani ga wasu daliban da Jami’ar Mustafa a jamhuriyar Nijar tare da halartar Ayatullah Ramezani babban sakataren majalisar Ahlul Baiti As ta Duniya.
-
Bidiyon Lokacin Da Aka Kori Jakadan Isra'ila Daga Jami'ar Senegal
Zanga-zangar da dalibai da malaman jami'ar Senegal suka yi ta tilastawa jakadan Isra'ila barin jami'ar.
-
Babban Sakataren Majalissar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya a Nijar:
Ayatullah Ramezani: Cikakken Musulunci Shi Ne Mabudin Hadin Kai Da Mutuntaka.
Ayatullah Ramezani ya yi bayanin ma'auni na cikkaken addinin Musulunci a wajen babban taron masu tabligi da daliban da suka kammala karatu a Jamhuriyar Nijar, inda ya jaddada hadin kan al'ummar musulmi, da martabar dan'adam, da fuskantar zalunci.
-
Hotuna | Babban Sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya Ya Gana Da Shugaban Darikar Tijjaniyya A Birnin "Kiota" Na Kasar Nijar.
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (A.S) da ya tafi kasar bisa goron gayyatar wasu malamai daga jamhuriyar Nijar, ya isa birnin "Kiota" na kasar Nijar. Bayan shiga birnin "Kiota", ya samu kyakkyawar tarba daga malamai da jama'ar wannan gari. Daga nan sai Ayatullah Ramazani ya gana da "Shekh Musa Abu Bakr Al-Hashimi" shugaban 'yan Tijjaniyya Qutb a birnin Quetta. A wannan taron, babban sakataren majalisar na Ahlulbaiti (AS) ya jaddada wajabcin hadin kai a tsakanin mazhabobin Musulunci.
-
Ziyarar Hadin Kai Da Ayatullah Ramazani Ya Yi Nijar; Tattaunawa Da Fitattun Malaman Yamai
Babban sakataren majalissar Ahlul Baiti (AS) ta duniya a wata ganawa da ya yi da limamin babban masallacin birnin Yamai, ya jaddada karfafa hadin kan Musulunci da goyon baya ga gudunmawar zamantakewar da malaman addini suke ga al’umma.
-
Labarai Cikin Hotuna | Na Isar Sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) Babban Birnin Nijar
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: Ayatullah Ramadani, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (A.S) ta duniya ya yi tafiya zuwa wannan kasa ta yammacin Afirka bisa gayyatar da wasu malaman addini daga kasar Nijar suka yi masa. A filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Yamai, wasu gungun malaman addini daga Nijar sun tarbi babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (a.s.) ta duniya.
-
Madagascar; Tsibiri Mai Tushen Musulunci Da Aka Manta Da Shi
Duk da tarihin Musulunci da ta ke da shi kasar Madagascar a yau na fadi ta shi wajen rasa asalin addininta. Tsibirin da mulkin mallaka ya mayar da addininta saniyar ware, amma al'adun Musulunci suna nan da rai a can.
-
Ayatullah Ramezani Ya Isa Ƙasar Nijar
Babban sakataren Majalisar Ahlulbaiti (AS) to duniya ya isa kasar Nijar