A yayin jawabinsa, Jagoran ya bayyana yadda Imam Khomaini ya samu kafircin duniya na ganin addinin Musulunci a matsayin kayan da, wanda ya taba mulkan duniya a baya, yanzu kuma lokacinsa ya wuce, amma ya fito da sabuwar Fikira na yunkurin dawo da ikon addini. Yace a lokacin ya zama har wasu daga Malamai da ke Makaranta (Hauza Ilmiyyah), suka rika ganin kamar wannan abinda Imam yake yi ya saba ma ka’ida, saboda yadda suka dauka aikin ma’abocin addini kawai shi ne ya yi karatu ya karantar, ba tare da ya yi magana akan siyasa ko gudanar da mulkin al’umma ba.
Shaikh Zakzaky ya bayyana yadda Imam Khomaini a lokacin yana makaranta (Hauza Ilmiyyah) ya fara sukan lamirin sarkin Iran na lokacin, wanda ake kira Shah. Inda ya kawo misalin wani lokaci da Sarki Shah ya je Hauza, duk Malamai suka mike masa saboda gudun cutarwarsa, amma Imam Khomaini shi bai mike ba. Da Shah ya hango Imam Khomaini yana zauna bai mike ba, sai ya je kusa da shi yace masa, bindigar da muka kashe ubanka tana nan. – Don uban Shah ya kashe uban Imam Khomaini. – Sai Imam (QS) yace masa, takalmin da muka jefi ubanka yana nan. – Domin baban Imam ya taba jifan uban Shah din da takalmi. “Wato in kun dawo, mu ma za mu dawo kenan".
Jagora ya bayyana cewa: “Shi Imam Khomaini (QS) Allah Ta’ala Ya sanya shi ya zama mutum ne wanda ke da natsuwa da kuma rashin tsoro, kuma yana magana fes dangane da nizamin Shah wanda ya sallama ma Amerika komai na kasar a lokacin".
Ya yi bitan irin takun da Amurka ke ma al’ummar Iran na mulkin mallaka kafin Imam Khomaini ya jagoranci juyin juya halin da ya kawar da Shah, ya kakkabe hannun Amurka daga dukiya da gudanarwar Iran.
Ya kuma nuna yadda Malamai a lokacin suka yi shiru kan duk irin barnar da ke faruwa a Iran, amma shi Imam Khomaini ne yake magana, cewa “ai dukiyar al’umman Iran ta al’ummar Iran ne ba ta Amerika ba, saboda haka don mene ne sarkin gari zai sayar da dukiyar al’umma ta hanyar sa Amurka ta zama tana biyan abinda ta ga dama.” A yayin da su kuma Malamai suna ganin bai kamata Imam ya rika irin wannan maganar ba. Har suka taba gindaya masa wasu sharudda cewa, ya daina sukan Amurka. Imam yace “ita Amerikan Sayyida Zahra ce da ba za a soke ta ba?” Har ta kai ga an kore shi, bayan kama shi da aka sha yi ana sakinsa.
Jagora (H) ya bayyana yadda aka rika sukan Imam Khomaini da rashin ilimi. Inda ya ba da misalin ilimin Imam Khomaini (QS) wanda a zamansa na Najaf a yayin gudun hijira ya rubuta littafi mai kunshe da batun cinikayya kadai mai manyan mujalladai har biyar. Yace: “Wannan ya nuna irin zarra da Imam yake da shi da zurfin ilimi, wanda (a karshe) suka sallama mashi akan cewa lallai ashe ba karamin mai ilimi ba ne".
Jagora ya yi bitan zaman Imam Khomaini (QS) a birnin Najaf a yayin gudun hijira, har zuwa lokacin da Sarki Shah ya ga tasirinsa na shiga cikin Iran daga nan ya sa aka kore shi, inda kasashen Larabawa suka dode masa damar shiga kasashensu, a karshe ya tafi Faransa da ta bashi mafaka.
Jagora ya kawo tarihin yadda Imam ya rika ganawa da dalibai ‘yan asalin Iran da ke karatu a Faransa, wanda suke zuwa wajensa su yi sallah tare da shi, ya gabatar musu da jawabi a dauka a kaset mai zare, sannan a buga wayar tarho irin ta da, a kunna jawabin, a dauka a Tehran ta wayar tarho din, sannan a gurza. Yace, ta haka ne duk sakon Imam ya rika yaduwa a wancan lokacin. Jagora yace, da ma yanzu ne shikenan baya bukatar wannan, sai ya yi magana ana kallonsa kaitsaye.
“Lokacin sai ya zama sakon Imam ya rika bazuwa, ya zama kaset din Imam ma farautan mutum ake yi idan an gan shi da shi, sai yadda ta yiwu kuma in aka kama mutum, ko a neme shi a rasa, ko ya dade ba a ganshi ba, saboda an haramta sauraron Imam. Saboda haka a boye mutane suke yada kasusuwan, a boye kuma suka sauraro… Amma duk da haka abin ana ta ji, kuma yana tasiri. Sakon dai shi ne, al’umma dole ta koma turban addini, dole kuma wannan zalunci da fasadi da ake yi ya kawo karshe, a koma nizamin addinin Musulunci".
Shaikh Zakzaky ya fadada bayani akan yadda Imam Khomaini ya fito da ‘concept’ din Wilayatul Faqih, wato shugabancin Malami, masani kuma mai tsoron Allah. “Tunda shugabanci ana ba mutum amana ne na jinainan mutane, da dukiyoyinsu, da mutuncinsu, (sai Imam ya kawo cewa); in kuwa haka nan ne, wanda ya fi dacewa ya rike wannan amanar, shi ne Malami mai tsoron Allah, wanda ya san cewa zai gamu da Allah gobe Kiyama, shi ne ya fi dacewa da ya rike amana, saboda haka shugabanci kamata ya yi Malami ya rike".
Yace: “Imam ya kawo ‘concept’ din shugabancin Malami, da kuma na komawa nizamin addini. Sai kuma wani ‘concept’ din ‘Intizar’, wato jiran bayyanar Imam Mahdi (AS)".
A nan ne Shaikh Zakzaky ya kawo wani hadisi da ke cewa “Mafificin aiki shi ne ‘intizar’.” Yace, ma’anar Intizar shi ne jiran Imam Mahdi (AS). “Intizari ba yana nufin ka tattare hannunka ka rike sai Imam ya zo sai ya kawo gyara ba ne, kamar yadda wasu suka dauka har yanzu. Akwai masu tunanin cewa sai randa Imam Mahdi (AS) ya zo sannan za a yi wani abu. Na’am, Imam Mahdi zai bayyana kamar yadda alkawari ne na Allah, ba fashi, in ya bayyana kuma addini zai tabbata a hannunsa. Amma ba yana nufin in ya bayyana shikenan sai komai ya yi daidai ba, za a fafata ne. Wato za a yi fada ne da nizamin da ya saba ma na Allah, amma shi Imam ne zai yi nasara. Wannan tabbas ne, don alkawarin Allah ne, shi ba za a fi karfinshi ba, shi ne zai fi karfi, saboda alkawari ne na Allah".
Yace: “To amma mene ne ma’anar jira? Wasu suna ganin jiran ne kawai, ka zauna sai Imam ya zo. A’a ba haka ba ne, za ka yi aiki ne, har ya zamana inda zai zo, zai samu dakaru a shirye".
Ya cigaba da cewa: “Kafin ma ya zo a bisa gaskiya ai an nuna ana ma fadan ne, ba sai ya zo ne za a fara fadan ba, in ana fadan ne al’ummar Musulmi sun shiga mawuyacin hali, a lokacin zai bayyana. To kun ga in ya bayyana zai zama akwai dakarunsa kenan a shirye, suna zaman jiransa ne kawai, da ya zo shi ne zai jagoranci wannan dakarun da dama akwai su, sai a cigaba da aiki. Inda kuwa tattara hannu za a yi, kun ga sai ya zo sannan za a fara kenan".
Shaikh Zakzaky ya nanata cewa: “Aiki za a yi don jiransa, shi yasa ma ya zo a ruwaya cewa, mafi girman aiki shi ne ‘intizar’. To kuma ya zai yi ya zama mafi wahalan aiki, idan ya zama tattara hannunka za ka yi ka zauna? In ka zauna ka yi shiru kace sai Imam ya bayyana, akwai wani wahala? Ai wannan bai da wani wahala. Tunda aka ce yana da wahala, ashe aiki ne mawuyaci. Aiki ne za ku yi tukuru domin bayyanarsa".
Jagora ya bayyana cewa, Imam Khomaini (QS) ya kawo sauyi a sauyi a fikiran mutane, da sauyi akan me ya kamata ya shugabanci mutane, kuma wa ya kamata ya shugabanci mutane, sannan meye ma’anar jira? Inda ya nuna jira yana nufin aiki ne gagarumi, kuma ya fara aikin. Sannan kuma ya kawo wani ‘concept’ na ‘Mustad’afin’, - wato raunana da ake fin karfinsu.
Yace: “Mustad’afin’ (raunanan) duniya tun a lokacin Imam (QS) suka fara ganin cewa lallai su ma sun yarda da wannan kira na Imam, na cewa lallai duk wanda ake zalunta dole a taimake shi. Saboda haka ma lokacin da ya ayyana ranar Quds ta duniya a ranar Juma’ar karshen Ramadan, sai ya zama har wadansu kasashe kamar Latin America, irin su Nicaragua, su ma suna yi, har ma yanzu ranar Quds ta duniya, kasashe da yawan gaske suna shiga ana yi da su, Musulmi da Kirista, har da Yahudu ma da basu yarda da mamaya ba, da ‘yan kwaminis. Wannan ‘concept’ din na kasancewa da wanda ake zalunta, ba da azzalumi ba, (Imam ne ya dago shi), a yayin da kullum jama’a suna ganin ka kasance tare da mai karfi ne don ka tsira".
Da yake bayani akan natijar samuwar Jamhuriyar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa: “Su Amerikawa ko ina sun je sun jijjibge sojo’jinsu, amma ba sojojin Iraan a ko ina a duniya in banda a cikin Iran, amma (Iran’) suna da makaman da za su har’bi ko ina a duniya daga cikin Iraan.” Ya kara da cewa: “Wannan duk natijar ‘revolution’ din ne, cewa sun mallaki kansu, kuma suna iya ma kansu komai".
Yace, daga natija din juyin kuma, shi ne samar da gwagwarmaya a sassan duniya. Shi ya samar da na Yemen din nan da ake gani. Na Hisbu* llah ba wanda ke musu, da na ‘yan gwagwarmayar Palas *dinu, duk ba wanda ke musu, amma yanzu na Yemen, -kasar da ta fi kowacce talauci a kasashen Larabawa, suka (kafircin duniya) far mata da harbe-har’be, suka yunwatar da mutane, sun yi barna a shekaru kamar goma da suka wuce a Yemen, suka yi ta ta yi, sai gashi yanzu Yemen ta gagare su, saboda haka sai suna jin haushin Iran. Saboda su Iran ba sayar da maka^mai suke ba, suna koya maka yadda za a ka yi ne".
“Yanzu sun gano cewa wannan juyi ya zo ya zauna ne. Da can tsoronsu kada ya bazu ya je sassan duniya. Amma yanzu anya akwai mai tunanin zai hana bazuwansa a sassan duniya? Bai riga ya bazu din ba? Ko da ma ba wai a kai muku mayaka, ko a koya muku dabarar ya’ki ba, a’a, kasantuwar tunanin mutum dangane da cewa wannan addini yana iya dawowa ya mallaki duniya, yanzu ya shiga ko ina. Kuma tunanin mutane dangane da karfin al’umma bayan sauran Iran sai ya zama ko ina suka gane ashe mutane suna da karfi”.
Jagora ya kawo irin yadda Imam Khomaini (QS) yake koyar da yin abu saboda Allah Ta’ala. Inda ya bayar da misalin da wani da ya je da wani attajiri gaban Imam a lokacin yana Faransa, yace masa wannan shi ne wane kaza, attajiri ne, kuma yana taimaka ma gwagwarmaya da dukiyarsa. Imam bai ce komai ba. Sai shi mutumin ya maimaita maganar; wannan attajiri ne mai suna wane, kuma yana taimakawa gwagwarmaya sosai. Sai Imam ya dube shi yace, me yasa ka maimaita maganar? Yace, ai na dauka baka ji ba ne. Sai Imam (QS) yace; “Idan yana yi don Khomaini ne, Khomaini ba ya ba da lada, in yana yi don Allah ne, Allah Ya sani".
Jagora yace, ta yiwu Imam ya san mutumin ne, amma dai akwai darasi a wannan, cewa ana yin abu ne don Allah. “Wannan kullum muna ta ma mutane magana akan haka, yi don Allah. In kana yi don Allah ne, Allah Ya sani, in ya so kar a sanka ma, kar ma a ji sunanka. In kuwa kana yi don ka shahara ne, ace kai ne wane kaza, shikenan, ladanka kenan ko ka zama wanen, ko baka zama wanen ba, iyakan ladan kenan”.
A karshen jawabinsa, Jagora ya bayyana yadda makiya suka yi ta kokarin ganin bayan juyin Musulunci na Iran tun a baya zuwa yanzu, amma Allah Ta’ala Ya hana su damar hakan. Sannan ya yi fata da addu’ar Allah Ya sa magajin Imam (QS), - wato Sayyid Ali Khamene’i (H) ya zama shi zai mika ‘raayar saurar’ Imam (QS) ga Imamul Hujja (AJ).
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
05/06/2026
08/12/1446H
Your Comment