Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya habarta cewa: An gudanar da wani gagarumin taro na malaman addinin Musulunci da daliban da suka kammala karatu a Nijar a birnin Yamai, wanda ya samu halartar shugabanin kungiyoyin Musulunci na Nijar da Qutb Tijjaniyya na Nijar. Babban bako na musamman a taron shi ne Ayatollah Reza Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (a.s.) na duniya.

29 Mayu 2025 - 11:16
Source: ABNA24

Your Comment

You are replying to: .
captcha