Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlulbaiti AS - ABNA - ya habarta cewa: an bude ofishin kamfanin dillancin labarai na ABNA a kasar Ghana tare da halartar babban sakataren Majalisar Ahlulbaiti AS ta duniya Ayatullah Reza Ramezani da kuma Hassan Sadraei Aref babban Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA. Ayatullah Ramezani ya yi tattaki zuwa wannan kasa ta yammacin Afirka tare da wata tawaga bisa gayyatar malaman addini daga Ghana.
Your Comment