27 Mayu 2025 - 22:57
Source: ABNA24
Ziyarar Hadin Kai Da Ayatullah Ramazani Ya Yi Nijar; Tattaunawa Da Fitattun Malaman Yamai

Babban sakataren majalissar Ahlul Baiti (AS) ta duniya a wata ganawa da ya yi da limamin babban masallacin birnin Yamai, ya jaddada karfafa hadin kan Musulunci da goyon baya ga gudunmawar zamantakewar da malaman addini suke ga al’umma.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (AWW) ta duniya da ya je kasar Nijar bisa gayyatar malaman addini ya gana da Sheikh Jibril Karanta shugaban kungiyoyin musulmin Nijar kuma limamin babban masallacin birnin Yamai.

A wannan ganawa da ya samu halartar gungun malamai daga jamhuriyar Nijar, Sheikh Jibril Krant ya mika godiyarsa ga Ayatullah Ramezani dangane da zuwansa a Yamai babban birnin kasar Nijar.

Babban sakataren majalissar Ahlul Baiti (AS) ta duniya ya jaddada batun hadin kan Musulunci a wannan ganawa da ya yi da Limamin babban masallacin Yamai.

Ayatullah Ramezani ya ci gaba da yabawa tare da gode wa Sheikh Jibril Karanta bisa yadda ya kula da lamarin iyali a Nijar, da magance matsalolin iyali da ke addabar al'ummar kasar, tare da taka rawa a matsayinsa na mafaka ga al'ummar Nijar.

A karshen wannan taro, babban sakataren Ahlul Baiti (AS) ya mika zoben Jagoran juyin juya halin Musulunci mai albarka ga Sheikh "Jibril Karanta", shugaban kungiyoyin Musulunci na Nijar kuma limamin masallacin Yamai.

Idan dai ba a manta ba, ganawa da malamai da masana da masu bincike da matasan kasar Nijar na daya daga cikin tsare-tsaren da babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ya yi a ziyarar da ya kai kasar.

Your Comment

You are replying to: .
captcha