28 Mayu 2025 - 22:30
Source: ABNA24
Bidiyon Lokacin Da Aka Kori Jakadan Isra'ila Daga Jami'ar Senegal

Zanga-zangar da dalibai da malaman jami'ar Senegal suka yi ta tilastawa jakadan Isra'ila barin jami'ar.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya habarta cewa, bisa wasu hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta na yanar gizo, Yuval Wax, jakadan kasar Isra'ila a kasar Senegal, an tilasta masa barin jami'ar Dakar, bayan da dalibai suka nuna rashin amincewarsu da zuwansa tare da rera taken nuna goyon baya ga Falasdinu.

An gayyaci jakadan na Isra'ila da ya yi jawabi a wani taro kan harkokin huldar kasa da kasa da aka gudanar a jami'ar Sheikh Anta Diop da ke kasar Senegal - babbar jami'ar ilimi mafi girma a kasar. To sai dai kuma da isarsa, dalibai da dama ne suka taru a wajen zauren taron suna rera taken "Yanci Ga Falasdinu" da "Yanci Ga Gaza" da cewa: "Isra'ila mai laifin yaki ce".

Hotunan bidiyo da aka yada ta yanar gizo sun nuna daliban suna daga tutocin Falasdinawa suna ta fadin suna yiwa sabon jakadan da aka nada eho, lamarin da ya hana shi yin magana.

Your Comment

You are replying to: .
captcha