11 Yuni 2025 - 22:46
Source: ABNA24
Ayarin Motocin "Gwagwarmayar Maghrib" Sun Isa Masaukin Farko A Libya + Hotuna

Ayarin motocin sun kunshi masu fafutuka sama da dubu da motocin safa 12 da kuma kananan motoci kusan 100. Bayan wuce garuruwa daban-daban a Tunisiya, ayarin motocin gwagwarmayar Maghreb za su isa Zirin Gaza ta hanyar Libiya da Masar.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: ayarin motocin ‘’Gwagwarmayar Magrib’ da daruruwan masu fafutuka daga kasashen Aljeriya da Tunusiya da Mauritaniya suka kafa da nufin karya kawanyar Gaza, sun isa tashar farko a birnin Zawiya na kasar Libya.

Tawagar ‘yan gwagwarmayar Magreb tare da halartar daruruwan masu fafutukar kare hakkin bil’adama daga Tunisia, Morocco, Algeria da Mauritania, sun taso ne daga babban birnin Tunisiya zuwa birnin Sousse, da nufin dakile kawanyar da aka yi wa Zirin Gaza.

Dr. Mohamed Amin Bennour, kakakin ayarin motocin ya bayyana a wata hira da ya yi da Anadolu cewa, manufar ayarin ita ce isa Gaza ta kasa da kuma isar da sakon "Zaluntar Falasdinu" ga kasashen duniya.

Har ila yau, ya jaddada cewa, jerin gwanon Gwagwarmayar Maghreb yana aiki tare da wasu shirye-shiryen kasa da kasa kamar "Tattakin Duniya zuwa Gaza" da "Freedom Flotilla".

Idan dai ba a manta ba ayarin motocin sun kunshi masu fafutuka sama da dubu da motocin safa 12 da kuma kananan motoci kusan 100. Bayan wuce garuruwa daban-daban a Tunisiya, ayarin motocin gwagwarmayar Maghreb za su isa Zirin Gaza ta hanyar Libiya da Masar. Ayarin dai wani shiri ne na duniya wanda ya hada da masu fafutuka daga kasashe sama da 30 na Turai da Kudancin Amurka da kuma kudu maso gabashin Asiya.

Dubban masu fafutuka daga kasashe 32 ne aka shirya za su hallara a mashigar Rafah a ranar 15 ga watan Yuni, kuma kungiyar masu fafutukar kare hakkin bil'adama za su hallara a birnin Alkahira a ranar 12 ga watan Yuni, su yi tattaki zuwa Rafah a wani tattaki na kwanaki uku.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha