30 Mayu 2025 - 13:52
Source: ABNA24
Ayatullah Ramazani Ya Isa Senegal + Hotuna

Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlulbaiti (AS) ya yi tafiya zuwa kasar Senegal bisa gayyatar da malaman addini suka yi masa daga cikin jerin kasashen da zai kai wa ziyara a kasashen Afirka.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa: Ayatullah Ramazani babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (AS) ya yi tattaki zuwa wannan kasa ta yammacin Afirka bisa gayyatar da wasu malaman addini daga kasar Senegal suka yi masa.

Ayatullah Ramazani Ya Isa Senegal + Hotuna

A filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Dakar, wasu gungun malaman addini daga kasar Senegal, da kuma jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Senegal, da mai ba da shawara kan harkokin al'adu na jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Senegal, da wakilin shugaban jami'ar Al-Mustafa a kasar Senegal, sun tarbi babban sakataren majalisar Ahlul-baiti As ta duniya.

Gholamreza Sharifi, mataimakin kodineta kuma darakta janar na majalisar Ahlul Bayt (AS), Dr. Abdul Hussein Kalantari, mai ba da shawara ga babban sakataren majalisar Ahlul Bait (AS), Hujjatul-Islam Wa Muslimeen Imamzadeh, darakta janar na kasashen Larabawa da Afirka na majalisar Ahlul Bayt (AS), Hassan Sadra'i Arif Shugaban tashar Ahlul Bayt (AS) ABNA, su suka yiwa Ayatullah Ramezani rakiya a wannan tafiya.

Ayatullah Ramazani Ya Isa Senegal + Hotuna

Ya kamata a lura da cewa ganawa da malamai, masu bincike, masana da matasan kasar Senegal na daya daga cikin tsare-tsaren da babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ya yi a ziyarar da ya kai kasar.

Your Comment

You are replying to: .
captcha