Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: Ayatullah Ramadani, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (A.S) ta duniya ya yi tafiya zuwa wannan kasa ta yammacin Afirka bisa gayyatar da wasu malaman addini daga kasar Nijar suka yi masa. A filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Yamai, wasu gungun malaman addini daga Nijar sun tarbi babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (a.s.) ta duniya.
Your Comment