2 Yuni 2025 - 10:04
Source: ABNA24
Sudan: Majalisar Ministocin Rikon Kwaryar Kasar Ta Rushe

A cewar rahotonnin safiyar yau Litinin daga kanfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) Idriss ya rusa majalisar ministocin kasar domin share fagen kafa sabuwar hukuma da majalisar ministoci.

A cewar rahotonnin safiyar yau Litinin daga kanfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) Idriss ya rusa majalisar ministocin kasar domin share fagen kafa sabuwar hukuma da majalisar ministoci.

Matakin na Idriss ya zo ne kwana guda bayan rantsar da shi a matsayin Firaministan Sudan. Firaministan Sudan ya sanar da matakin rusa majalisar ministocin ga mambobin gwamnatin kasar tare da neman shugabannin ma'aikatun kasar da su tafiyar da harkokin kasar har sai an kafa sabuwar majalisar ministoci.

Kamar dai yadda aka sani an rantsar da sabon Firaministan Sudan Kamel Idriss a ranar Asabar a gaban Abdel Fattah al-Burhan, shugaban majalisar mulkin kasar kuma babban kwamandan sojojin Sudan.

Bayan rantsuwar, sabon firaministan na Sudan ya jaddada cewa, zai ba da duk lokacinsa da kokarinsa wajen tabbatar da rayuwa mai inganci ga 'yan kasarsa.

Nadin sabon firaminista ya zo ne bayan da tsohon Firaministan Sudan Abdullah Hamdok ya yi murabus daga mukaminsa kimanin shekaru hudu da suka gabata, inda ya bar mukamin firaminista.

Idris dai jigo ne a harkokin diflomasiyya a Sudan kuma yana da tarihin shiga tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a rikicin kasar. Ya kuma wakilci Sudan a taron kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Yakin basasar Sudan ya fara ne a watan Afrilun shekarar 2023 tare da kara tada jijiyoyin wuya tsakanin sojojin Sudan da dakarun gaggawa na "Mohammed Hamdan Daqlo", wanda aka fi sani da "Hamidati". A watan Janairun bana ne aka sanyawa Daqlo takunkumi saboda aikata laifukan yaki a Sudan. A baya dai Hamidati ya raba madafun iko da sojoji da ‘yan siyasa farar hula a wani bangare na yarjejeniyar siyasa na kafa gwamnati bayan hambarar da tsohon shugaban Sudan Omar Al-Bashir a shekara ta 2019.

Kungiyoyin soji biyu sun kori ‘yan siyasa farar hula a wani juyin mulki a watan Oktoban 2021, kuma kwamandan sojoji Janar Abdel Fattah al-Burhan ya karbi ragamar gwamnati. Sai dai kuma daga baya kungiyoyin sojojin sun shiga cikin yakin basasa wanda ya haifar da barna mai yawa tare da haifar da mummunar matsalar jin kan dan Adam da yunwa a yankuna daban-daban na kasar Sudan.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha