28 Mayu 2025 - 18:24
Source: ABNA24
Ayatullah Ramezani: Cikakken Musulunci Shi Ne Mabudin Hadin Kai Da Mutuntaka.

Ayatullah Ramezani ya yi bayanin ma'auni na cikkaken addinin Musulunci a wajen babban taron masu tabligi da daliban da suka kammala karatu a Jamhuriyar Nijar, inda ya jaddada hadin kan al'ummar musulmi, da martabar dan'adam, da fuskantar zalunci.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: an gudanar da babban taron malaman addinin muslunci masu tabligi da daliban da suka gama karatu na jamhuriyar Nijar a birnin Yamai babban birnin kasar, tare da halartar shugabanin kungiyoyin addinin musulunci na wannan kasa da kuma na darikar Tijjaniyya ta Nijar. Babban babban bako na taron shi ne Ayatollah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya.

A farkon jawabinsa a wajen taron, Ayatullah Ramezani ya jaddada abubuwan da musulmi suka hada musulmai a tsakaninsu kamar aikin Hajji da kuma abubuwan da suka hada da Iran da Nijar, ya ce: Wajibi ne mu yi koyi da abin da ya faru na yanka Isma'il. Babban darasin wannan lamari shi ne tauhidi, walau tauhidi a karance ko tauhidi a aikace. Imam Khumaini (R.A) shi ne ma'auni na yakar shirka a wannan zamani, kuma ya sanya musulmi a duniya sun zamo masu daraja.

Cikakken Musulunci; Mahangar Imam Khumaini (RA) Game Da Addini

Babban Sakataren Majalissar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya ya dauki Imam Khumaini (RA) a matsayin mai kira zuwa ga cikkaken Musulunci, ya kuma bayyana cewa: Marigayi Imam ya yi imani da cewa ya kamata a rika dubi ga Musulunci da zurfinsa, ba wai sama-sama ba. A mahangarsa, Musulunci yana da na waje yana da na ciki, daukaka da kyau, kuma cikakken Musulunci ya kunshi dukkan wadannan bangarori. Imam Khumaini (RA) ya kira mu baki daya zuwa ga kafa al'ummar musulmi. Ya kira mu zuwa ga yunkurawa ta daidaiku da ta zamantakewa da kuma hada kai. Abin da ke cikin sakon marigayi Imam shi ne cewa a kiyaye mutuncin dan Adam kowane irin launi, jinsi da harshe, kuma kada a zalunce kowa.

Da yake bayyana cewa kur'ani mai tsarki ya jaddada ka'idoji guda biyu na asali, mutuntaka da adalci, ya kara da cewa: Kiran Imam Khumaini (RA) da Imam Khamene'i shi ne cewa kada mu zalunci wani ko kuma mu yarda da zaluncin wani. Don haka dalilanmu da dabi'unmu da addininmu sun yi nuni da cewa idan a wani lungu na duniya aka kashe yara da mata da zalunci, mu tashi tsaye wajen yakar wannan zalunci, mu mai da martani. A kasashen Turai da Amurka su ma sun mayar da martani kan wannan zaluncin, shin ba za mu mayar da martani ga wannan zalunci ba?

Ayatullah Ramazani ya ci gaba da cewa: Wajibi ne mu yi koyi domin Allah, mu koyar domin Allah, mu yi aiki domin Allah. Idan wani ya yi haka, kamar yadda hadisi ya nuna, wannan mutumin za a kira shi “Babba” a masarauta Alllah Ta’ala.

Farko Yin Ilimi Sai kuma yin aiki da shi; haske ga zukatan masu Tabglilin Addini

Babban Sakataren Majalissar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya ya yi nuni da nau’o’in ilimi: Muna da ilimi nau’i biyu, ilimi wanda dole ne mu koya kuma mu neme mu same shi, amma dayan ilimin shi ne ilimi bayan aiki. Ayatullahi Bahjat ya jaddada bukatar ilimi bayan aiki, sannan ya yi ishara da hadisin da ke cewa idan wani ya yi aiki da abin da ya sani, Allah Ta’ala zai koya masa abin da bai sani ba. Wannan ilimin haske ne kuma yana haskakawa. A tafsirin Imam Sadik (AS) ilimi ba wai yawan karantarwa da ilmantarwa ba ne, illa dai ilimin haske ne wanda zuciyar dan Adam ke haskakawa da shi.

Ya dauki sharadin samun nasara wajen wa'azin isar da sakon addini ta hanyar kula da ladubba guda uku sannan ya fayyace su da cewa: Ladabi na farko shi ne yin ladabi tare da Rai, ma'ana mu kasance masu ladabi ga kanmu. Dabi’a ta biyu ita ce yin Ladabi tare da wasu, ma’ana dangantakarmu da wasu ta zama kyakkyawa. Ladabi na uku shi ne yin ladabi tare da Allah, ma’ana a cikin alaqarmu da Allah, mu kiyaye ladubbanmu, mu daukar Allah a matsayin mahalicci, mai tarbiyantarwa, masoyi, abun kauna, da sauransu.

Ayatullah Ramazani da yake bayyana cewa wa'azi na daya daga cikin siffofin annabawan Ubangiji, Ayatullah Ramazani ya jaddada cewa: Ba wai kawai mai wa’azi yana isar da Magana ne ba. Don haka dole ne ya san gaskiya ta yadda zai isar da ita cikin zukatan masu sauraro. Dangane da haka ne Manzon Allah (SAW) ya dauki zukatan mutane wajen yin wa’azi. Haka kuma kowane mai wa’azi yana da wasu mukamai guda biyu, wadanda kuma dukansu na annabawa ne. Na farko, kowane mai wa’azi malami ne. Na biyu, kowane mai wa’azi mai bayar da tarbiya ne. Don haka dole ne kowane mai wa’azi ya kasance yana da yanayi na Ubangiji kuma ya isar da wannan yanayin Ubangiji ga mai sauraro.

Bayar Da Amsa Ga Shakkun Kasashen Yamma; Nauyin Da Yau Hau Kan Bangaren Isar Da Sako A Yau

Babban Sakataren Majalissar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya ya yi ishara da siffofin masu wa’azi: Wajibi ne masu wa’azi su san masu sauraronsu kuma su san abin da za su gabatar a cikin ko wane yanayi. Aikin mai wa’azi sannu a hankali yake gudana kuma dole ne ya yi aikin koyarwa sannu a hankali. Dole ne mai wa’azi ya yi magana ta yadda shi kansa da masu sauraro suka fahimci maganar. Bai kamata mai wa'azi ya gabatar da addinin Musulunci a iya zahiri ba, don haka karatunsa ya wadace shi ta yadda zai amsa tambayoyin masu saurarensa.

Ya kara da cewa: kasashen Yamma a kai a kai suna haifar da shakku da yawa a yau, misali, wannan shakku ya taso a yammacin duniya cewa dan Adam baya bukatar addini don kaiwa ga kamalar ruhiyya. Don haka ya zama wajibi mu gabatar da addinin Musulunci daidai kuma cikakke mai zurfi. Mun yi imani cewa Musuluncin Muhammadu (SAW) ba Musuluncin ta’addanci da tashin hankali ba ne. Mutane da yawa sun gaya wa Manzon Allah (SAW) ranar da aka ci Makka cewa mu ramuwar gayya, amma Manzon Allah (SAW) ya ce yau ranar rahama ce.

Ayatullah Ramezani ya dauki rahamar Musulunci a matsayin dalilin yaduwarsa duniya sannan ya ce: Dabi’un Manzon Allah (SAW) ne ya sanya Musulunci ya mamaye duniya. Da Manzon Allah (SAW) yana raye, da dukkan ku masu tabligi da ke Nijar, wanda dukanku daga jinsin Bilal ne, da kun kasance cikin rukuninsa na farko masu isar da sako a yau.

A bangare na karshe na wannan taro, an sanyawa wasu dalibai daga daliban jami’atul Mustafa da ke jamhuriyar Nijar rawani da yaye wasu dalibai d suka gama karatunsu a jami’ar a gaban Ayatullah Ramezani, Babban Sakataren Majalissar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya

Your Comment

You are replying to: .
captcha