Hotuna: Taron "Gudunwar Malaman Musulunci A Ci Gaban Duniya Tare Da Mai Da Hankali Kan Falasdinu" Da Aka Gudanar A Babban Birnin Kasar Senegal.
Kamfanin Dillancin Labarai na AhlulBaiti: An gudanar da taron "Gudunwar Malaman Musulunci a Ci gaban Duniya tare da mai da hankali kan Falasdinu da kuma bayyana shirin jagoranci na makomar Palastinu" a Dakar babban birnin kasar Senegal. A cikin wannan taro, Majid Rezaei, shugaban sashen Afirka na Majalisar Ahlulbaiti (a.s.) ta duniya ya gabatar da bayani yanayi da halin da ake ciki a Gaza da Palastinu, ya kuma yi ishara da ra'ayin Jagora kan wajabcin gudanar da zaben raba gardama tsakanin al'ummar Palastinu. Dr. Abdul Hussein Kalantari mai ba da shawara ga babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (a.s) ta duniya ya kuma jaddada laifukan gwamnatin sahyoniyawan a Palastinu da kuma bukatar hadin kan musulmi wajen fuskantar kasar Isra'ila.
Your Comment