7 Yuni 2025 - 23:20
Source: ABNA24
An Bude Ofishin Yada Labaran ABNA A Ghana / ABNA Ta Zama Muryar Ahlul Baiti (AS) a Yammacin Afirka

An bude ofishin ABNA a nahiyar Afrika a babban birnin kasar Ghana a wani biki da ya samu halartar babban sakataren majalissar Ahlul Baiti (AS) ta duniya.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA – ya habarta cewa: an gudanar da bikin bude ofishin yankin Afirka na ABNA a kasar Ghana a birnin Accra fadar mulkin kasar Ghana, tare da halartar Ayatollah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul Baiti (AS).

A nasa jawabin shugaban jami'ar musulunci ta kasar Ghana Hujjatul-Islam Kamal Ezzat ya sanar da bude ofishin yada labarai na ABNA kashi na farko, yana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na bunkasa koyarwar Ahlulbaiti (AS) a yammacin Afirka.

Yayin da yake ishara da kayayyakin da aka samar a jami’ar, a wajen bikin bude wannan ofishin, ya ce: Ofishin dakin watsa labarai na jami’ar Musulunci ta Ghana ya kunshi dakuna guda hudu da suka samar da kayayyakin more rayuwa don ci gaban harkokin yada labarai.

Ezzat ya kara da cewa: A yau, muna kaddamar da kashin farko na ofishin kamfanin dillancin labarai na ABNA da ke Ghana tare da halartar jami’ai da malaman addini.

Shugaban Jami'ar Musulunci ta Ghana ya ci gaba da bayanin ma'auni na aikin: Kashi na farko shi ne samar da wani tushe a hukumance kuma tsayayye domin gudanar da harkokin yada labarai a tafarkin yada koyarwar Ahlul Baiti (AS), kuma in sha Allahu kashi na biyu zai hada da kaddamar da gidan rediyo da talabijin na intanet.

Daga karshe ya jaddada cewa: Burinmu shi ne samar da fili ga dukkan malamai masu tabligi, manyan malamai da masu fafutuka masu sha’awar tafarkin Ahlulbaiti (AS) ta yadda za su bunkasa ayyukansu na isar da sakon addini yadda ya kamata a yanayin zamani.

Kafofin Watsa Labarai; Kayan Aiki Don Tabbatar Da Juyin Juya Halin Musulunci A Duniya

A nasa jawabin a wajen bikin, Amir Heshmati mai ba da shawara kan harkokin al'adu na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi ishara da irin rawar da kafofin watsa labarai suka taka a tarihi wajen cin nasarar juyin juya halin Musulunci tare da jaddada muhimmancin samar da ruwayoyi da kuma samar da abubuwan da kafofin watsa labarai ke da shi don karfafa maganganun Musulunci da koyarwar Ahlulbaiti (AS).

A farkon jawabin nasa ya bayyana cewa: “A lokacin da nake dalibi na gudanar da bincike a fagen yada labarai, inda muka kammala shi da cewa Imam Khumaini (RA) ya gudanar da kusan kashi 75 cikin 100 na hirarrakinsa da ayyukan watsa labarai a garin Noufal-Le-Chateau, wanda hakan ke nufin cewa rabin karni da suka gabata ya fahimci muhimmancin kafafen yada labarai wajen ciyar da manufofin juyin juya halin Musulunci gaba.

Mai ba da shawara kan harkokin al'adu na kasar Iran ya kara da cewa: Tare da fahimtar lokaci da wuri, marigayi Imam ya shirya hirarrakin Noufal-Le-Chateau a wani wuri da ya dace a nahiyar Turai, kuma tattaunawar ta zama wani muhimmin al'amari na dunkulewar sakon juyin juya halin Musulunci a duniya.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da halin da kafafen yada labarai ke ciki a duniya, Heshmati ya kuma bayyana cewa: A yanzu da kowa ya san muhimmancin kafafen yada labarai, ayyukan watsa labarai da gabatar da ingantattun ruwayoyi na iya yin tasiri matuka wajen ciyar da manufofin majalisar Ahlul Baiti (AS) gaba da karfafa hadin kai da wayar da kan musulmi a fadin duniya.

Dandalin Muryar Zaman Lafiya Da Adalci Da Imani

Hassan Sadrai Aref, babban darakta na kamfanin dillancin labarai na ABNA, shi ma ya sanar da bude sabon ofishin wannan kafar yada labarai a babban birnin kasar Ghana a wannan biki, ya kuma bayyana cewa: Muna farin cikin sanar da bude ofishin kamfanin dillancin labarai na ABNA a birnin Accra domin karfafa al'adun imani da zaman lafiya da adalci wadanda suka samo asalin tushe daga koyarwar Musulunci da mazhabar Ahlul Baiti (AS).

Ya kara da cewa: Wannan ofishi na iya share fagen gabatar da tunaninnika, ayyuka da karfin matasa, masana da cibiyoyin al'adu da zamantakewa a yankin Afirka ta Yamma da kuma samar da kafar buga labarai masu inganci, masu dacewada fatan alheri.

Manajan daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA, yayin da yake ishara da yadda wannan kafar yada labarai ta kasa da kasa, ya bayyana cewa: Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA a halin yanzu yana aiki a harsuna 27 na duniya, da suka hada da Larabci, Turanci, Swahili, Hausa da Fotigal, kuma muna fatan wadannan ayyuka za su kara fadada, da kwarewa, da zamanantarwa da inganci a kowace rana.

Sadraei Aref ta kammala da jaddada cewa: Za'a iya cimma wadannan manufofin tare da goyon baya da hadin kan 'yan'uwa mata masu hazaka a yankin yammacin Afirka, kuma muna da kyakkyawan fata ga makomar wannan tafarki.

Ahlul Baiti (AS); Abin Koyi Ga Dukan Adam

Har ila yau, Ayatullah Ramazani ya bayyana kafa ofishin kamfanin dillancin labarai na ABNA a kasar Ghana da manufofinsa, inda ya bayyana cewa: Ina fatan kafa wannan ofishin zai zama alheri kuma zai zama wani sabon fagen yada labarai. Tabbas, kafa ofishin kamfanin dillancin labarai na ABNA a Ghana na iya taka muhimmiyar rawa, da farko, ga gwamnatin Ghana. Abin da muka fi maida hankali da shi a cikin layin labarai don samar da batutuwa a Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA, shine hangen nesa na hankali, ruhiyya, mutuntaka da adalci, kuma wannan shine abin da duniya ke nema. Ya kamata al'ummar ɗan adam su sami damar yin amfani da ƙa'idodi na zinariya kamar mutunci da ruhiyya waɗanda dukan ɗan adam ke kishirwarsu. Muna jaddada kyawawan dabi’u da halayya na yada labarai a Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA, don haka samar da labarai da wannan kamfanin dillanci ya yi a Ghana zai yi amfani ga kasar nan.

Da yake bayyana cewa daya daga cikin manufofin kamfanin dillancin labarai na ABNA shi ne wayar da kan masu saurare da cibiyoyi da kuma mutane masu fafutuka a fagen bunkasa koyarwar Ahlul-Baiti (AS), ya kara da cewa: Yana da muhimmanci a gabatar da Ahlul Baiti (AS) ga fitattun al'ummar Ghana da ma daukacin Afirka baki daya, Ahlul Baiti (AS) sun kasance fitattu kuma abin koyi ga bil'adama. Ba wai kawai Imamai ma’asumai (AS) sun zama abin koyi ne na ‘yan Shi’a ba, sai dai su abin koyi ga dukkan musulmi da dukkanin mabiya addinai da kuma dukkan bil’adama Ahlul-baiti (AS) ba su koya mana wani abu ba face mahangar bil’adama, mahanga ta ilimi da gaskiya, mahanga ta cikar halitta, da mahanga ta ruhi da adalci”.

Babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti ta duniya ya dauki al'ummar bil'adama a matsayin masu bukatuwa da lamurra da Imamai ma'asumai (AS) suka jaddada, ya kuma bayyana cewa: Babu shakka wadannan koyarwa za su iya taka rawa wajen ci gaban kasa. Idan ƙasa tana son girma, kimiyya da ilimi a gefe guda, kuma imani da ruhiyya, haɓaka imanin ɗan adam, da alaƙa da duniyar gaibi da gaskiyar rayuwa, na iya taimakawa wannan haɓakar.

...................................

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha