Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya habarta cewa: an gudanar da bikin yaye dalibai a jami'ar Al-Mustafa da ke jamhuriyar Nijar a birnin Yamai fadar mulkin jamhuriyar Nijar, tare da halartar Ayatullah Ridha Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya. Ayatullah Ramazani ya yi tattaki zuwa wannan kasa ta yammacin Afirka bisa gayyatar malaman addini daga Nijar.

29 Mayu 2025 - 11:35
Source: ABNA24

Your Comment

You are replying to: .
captcha