Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa: Ayatullah Reza Ramezani babban sakatare na majalisar Ahlulbaiti (AS) tá duniya ya isa jamhuriyar Nijar da ke yammacin Afirka bisa gayyatar malaman addini. Wasu gungun malaman addini daga Nijar sun tarbe shi a filin jirgin sama na Yamai.
Ya kamata a lura da cewa ganawa da malamai da masana da masu bincike da kuma matasan kasar Nijar na daya daga cikin tsare-tsaren da babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya zai yi a ziyarar da ya kai kasar.
Your Comment