Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya habarta cewa: Malaman addini na kungiyar sasantawa da zaman lafiya ta kasar Tanzaniya JMAT sun bayyana matukar bakin cikin su dangane da matakin da wasu matasan kasar Kenya suka dauka na rashin mutunta shugabar kasar Tanzaniya, Dr. Samia Suluhu Hassan.
Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban JMAT, Sheikh Dr. Alhad Mussa Salum, ya ce irin wadannan maganganu da ayyukan ba na mutunci ba ne kuma suna barazana ga hadin kai da fahimtar juna tsakanin kasashe makwabta da abokan arziki.
Sheikh Dr. Had y ace: "Lokacin da muka isa, kura takai bango, abu yayi tsamari, ba za mu iya yin shiru ba idan muka ga ana wulakanta shugabanninmu ba tare da wani dalili ba".
A nasa jawabin, Sheikh Dr. Alhad ya bukaci shugaba Samia Suluhu Hassan da ya yafe wa matasan da suka aikata laifin, inda ya ce matasan sun yi kuskure amma duk da haka suna da damar koyo da gyara halayensu.
Shugabannin addinai na JMAT sun yi Allah wadai da matakin da matasan Kenya ke yi na rashin mutunta shugaban kasar Tanzaniya, Hon. Dr. Samia Suluhu Hassan
"Muna rokon Honarabul Samia Suluhu Hassan da ta gafarta wa matasan Kenya da suka raina ta, mun yi imanin ba su fahimci girman abin da suka yi ba." Inji Sheikh Dr. Alhad Mussa Salum, wanda shine Shugaban JMAT-TAIFA.
Gabaɗaya, shugabannin JMAT sun kuma yi kira ga matasan gabashin Afirka da su mutunta shugabanni, su tabbatar da cewa banbance-banbancen siyasa ko zamantakewa ba su haifar da ƙiyayya, ba'a ko rashin mutuntawa ba.
Mun sanya wasu hotuna a kasa na taron shugabannin addinai na kungiyar sulhu da zaman lafiya ta Tanzaniya, karkashin jagorancin shugaban kungiyar sasantawa da zaman lafiya ta Tanzania (JMAT-TAIFA), Sheikh Dr. Alhad Mussa Salum, da babban sakataren JMAT-TAIFA, Bishop Dr. Gabriel Ole Maasa.

















Your Comment