30 Mayu 2025 - 16:19
Source: ABNA24
Ayatullah Ramezani A Dakar: Koyarwar Ahlul Baiti (AS) Ita Ce Hanyar Zuwa Ga Ubangiji

Babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ya bayyana hakan a wajen taron makokin shahadar Imam Jawad (AS) da aka gudanar a babban birnin kasar Senegal cewa: “Yin amfani da koyarwa da maganar Ahlulbaiti (AS) yana taimaka mana wajen kusantar Allah ta hanya ta yin aiki, koyarwar Ahlul Baiti (AS) ta tauhidi ce, bisa dabi’a, kuma bisa ga hankali”.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa: an gudanar da zaman makokin shahadar Imam Jawad (AS) tare da halartar iyalan gidan Iraniyawa mazauna kasar Senegal a dakin taro na al'adun Imam Riza (AS) da ke Dakar babban birnin kasar Senegal.

Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (AS) wanda ya yi tattaki zuwa wannan kasa bisa gayyatar malaman addini daga kasar Senegal, ya halarci taron a matsayin mai jawabi na musamman.

Har ila yau a wajen taron akwai Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Senegal, da mai ba da shawara kan harkokin al'adu na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Senegal, da shugaban jami'ar Al-Mustafa da ke kasar Senegal, da wakilan ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Senegal, da wasu wakilan tattalin arziki na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Senegal, da wasu jami'an Majalisar Ahlul Bait (AS) ta duniya da dama.

A cikin jawabinsa yayin da yake ishara da sifofin koyarwar Ahlulbaiti (AS), Ayatullah Ramezani ya bayyana cewa: Yin amfani da koyarwa maganganun Ahlulbaiti (AS) yana taimaka mana wajen samun kusanci ga Allah a aikace. Koyarwar Ahlul Baiti (AS) ta Tauhidi ce, bisa dabi’a, kuma ta dace da hankali.

Siffofin Mumini Guda Uku Masu Muhimmanci A Mahangar Imam Jawad (AS).

Babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (AS) ya bayyana cewa, kamar yadda aka ruwaito daga Imam Jawad (AS) mumini yana bukatar siffofi guda uku, yana mai cewa: Siffa ta farko da aka ambata a cikin wannan ruwaya ita ce (samun dace daga Allah). Wasu mutane suna da lokaci, amma ba su samin dacewa da yin ibada. Ya kamata kowa ya nemi abubuwan da ke hana samun dacewar Ubangiji a cikinsa. A addu'ar Sabah (addu'ar da ake karantawa duk safiya da aka ruwaito daga Imam Ali As) yazo cewa: Ya Ubangiji idan baka bani dacewa ba, to Bazan iya samun tafarki madaidaici ba.

Ya ci gaba da cewa: Siffa ta biyu da aka ambata a ruwayar Imam Jawad (AS) ita ce mumini (mai wa’azi ne ga kansa). Wasu ba su da juriyar nasiha ga wasu, amma dole mumini yayi nasiha ga kansa. Ɗaukar nasiha daga wurin wasu na daga cikin halayen Malamai da manyan mutane a tarihin Musulunci. Ko da ba mu da wannan ruhun, dole ne mu sami mai wa’azi a cikin kanmu wanda zai yi mana gargaɗi.

Ayatullah Ramezani yana ganin karbar nasiha daga wasu a matsayin daya daga cikin siffofin mumini kuma ya fayyace cewa: Imam Jawad (AS) ya ambace shi a cikin ruwayarsa (kuma ƙarba da yarda daga wanda yayi masa nasiha) a matsayin sifa ta uku ta mumini, ma'ana wajibi ne mumini ya karbi nasihar wasu. Idan muna da wadannan siffofi, za mu yi nasara wajen samar da ayyuka masu girma ga addinin Allah. Tabbas akan wannan tafarki babu shakka zamu fuskanci matsaloli masu yawa kuma dole ne mu yi hakuri.

A bangare na karshe na taron, babban malamin addinin Ahlulbaiti (AS) Malam Ali Hashemi ya gabatar da jawabai na juyayin shahadar Sayyid Imam Jawadul-Aimmah (AS).

Your Comment

You are replying to: .
captcha