-
Labarai Cikin Hotuna | Almajiran Sheikh Zakzaky H Sun Fara Tattaki Daga Najaf Zuwa Karbala
Kamfanin Dillancin Labarain ƙasa da ƙasa Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: yan sa'o'i da suka gabata 'Ƴan'uwa almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) masu gudanar da ibadar tattakin Arba'in na Imam Husain (A.S) sun kama hanyar Karbala daga birnin Najaf. A yau Asabar 14/Safar/1447 (09_08_2025). Iraq Media Forum. 09_August_2025 14_Safar_1447H
-
Sheikh Ibrahim Alzakzaky {H}: Mutum Ya Tsaya Ƙyam Tsakani Da Allah, Ƙyam Saboda Allah, Ko Me Zai Faru Ya Faru.
Jagora ya gana da ba'adin 'yan uwa a Asabar 9 ga Almuharram 1447 a gidansa da ke Abuja, a munasabar juyayin Shahadar Abi Abdullahil Husain (AS).
-
Katsina Najeriya: An Gudanar Da Muzaharar Ashura + Hotuna
Da misalin ƙarfe 4:00pm na yammacin yau Lahadi 10 ga watan Muharrama, 1447 dai-dai da 06/07/2025 ne ’yan’uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) na Da’irar Katsina suka fito ƙwai da kwarkwata domin bin sahun muminai na faɗin duniya mabiya mazhabar Ahlulbaiti (S) wajan nuna alhini da juyayi na kisan jikan Annabi Muhamamd, Imamul Husain (A.S).
-
Sheikh Ibrahim Alzakzaky {H}: Allah Ta'ala Yayi Imam Khumaini (QS) Mutum Wanda Ke Da Natsuwa Da Rashin Tsoro
A ranar Talata 3/6/2025 (6/12/1446) ne Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabi ga dalibai da malaman manyan makarantu da ke karkashin inuwar ‘Academic Forum’, a munasabar tunawa da shekara 36 da wafatin Imam Khumaini (QS), a gidansa da ke Abuja.
-
Najeriya Ta Karbi Bakuncin Taro Kan Gudunmawar Imam Khumaini Da Tasirinsa A Afirka + Bidiyo
A jiya Lahadi ne aka gudanar da wani taro a birnin Kano da ke arewacin Najeriya domin yin nazari kan rayuwa da kuma gudunmawar marigayin wanda ya kafa jamhuriyar Musulunci ta Iran Imam Khumaini. Kungiyar Zahra ta Najeriya, tare da hadin gwiwar jami’ar Ilimi ta AlMustafa da ke Kano, da kungiyar Academic Forum na Harkar Musulunci ne suka shirya taron.
-
Sheikh Ibrahim Zakzaky {H} Ya Gana Da Ƴan Uwa 33 Da Aka Sako Daga Gidan Yari
Da safiyar jiya Alhamis 1 ga watan Zulhijja, 1446 (29/5/2025) ne Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya gana da ragowar ‘yan uwa mutum 33 da suka fito daga kurkuku, bayan shafe kimanin shekaru shida suna tsare tun bayan waki’ar 22 ga July 2019 a Abuja.
-
Sheikh Yakubu Yahaya: Hatta Waƙi'ar Buhari Ba Ta Iya Raba Ƴan Uwa Da Jagoranci Ba
Sheikh Yaqoub ya ƙara jaddada cewa, ‘yan uwa a cikin Harka na da manyan hadafi guda biyu: Na farko, mutum ya samu tsira a gaban Allah (SWT) ta hanyar sauke nauyin da aka ɗaura masa. Na biyu kuma, shi ne samun ƙiyadar jagoranci ba tare da rarrabuwa ba koda kuwa an samu bambance-bambancen fahimta ko ra’ayi.
-
Shaikh Zakzaky H Ya Gana Da Ɗaliban Fudiyyah + Hotuna
Jiya laraba 23 ga watan DhulQa'ada, 1446H (21/05/2025) Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), kamar yadda aka saba kowacce shekara ya gana da wasu daga cikin ɗaliban makarantun Fudiyya daban-daban waɗanda suke shirin yin bikin haddar Alkur’ani Mai girma, a gidansa da ke Abuja.
-
Lebnon: Isra’ila Ta Kai Hari Kan Wata Mota Mutun Daya Yayi Shahada
Mamaya na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Lebanon daga lokaci zuwa lokaci ta hanyar kai hare-hare tare da kashe 'yan kasar ba tare da hukuma ta dauki wani mataki ba.
-
Fitattun Abubuwan Da Suka Faru A Kisan Kiyashin Da Isra'ila Ke Yi A Gaza A Rana Ta 577
Dakarun mamaya na Isra'ila na ci gaba da kisan kare dangi a zirin Gaza, bayan sun ci gaba kisansu tun kwanaki 49 da suka gabata da kuma kwanaki 577 da fara kai farmakin Guguwar Aqsa. Hakan ya biyo bayan sabawar da Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, tare da goyon bayan da Amurka ke yi na siyasa da soji, a yayin da kasashen duniya suka yi shiru da kuma watsin da ba’a taba ganinsa a kasashen duniya ba.