Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: An fara muzaharar Maulidin a cikin wani anguwa mai suna Fish Market dake Apo" sannan aka fito da muzaharar zuwa wani babban junction inda anan aka rufe, bayan kammala muzaharar yan'uwa sun fara watsewa sai ga jami'an tsaro mota biyu Mopol da police suka fara wuce 'yan uwa sai suka samu wani waje suka tsaya suka fara harbi da harsasai masu rai.
Zuwa hada wannan rahoton bamu da tabbacin wanda aka harba, ko aka kama" abun da muka sani anyi muzaharar Maulidin Manzon Allah (S.A.W.W) a Abuja, koda Azzalumai basu so ba.
Mai Rahoto: Isa Charis
AliAssajjad Ibn Taheer
10th/Sept/2025











Your Comment