A ranar Laraba, 17 ga Rabi’ul Auwal, 1447, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da ‘yan uwa dalibai da ke karatu a jami’o’i daban-daban a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ganawar, wadda ta auku a irin ranar Mauludin Manzon Rahma (S) na wannan shekarar, ta auku ne a Tehran, babban birnin Iran, biyo bayan kammala taron makon hadin kan Musulmi, wanda “Majma’ut Taqrib Bainal Mazahib” ta shirya a karo na 39, da kuma taron gangamin goyon bayan Palasdinawa da “Majalisar Kasa da Kasa na Farkawar Musulunci” ta gabatar a Tehran.
A yayin jawabinsa ga daliban, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana dalilin kasancewarsa a Jamhuriyar Musulunci a daidai wannan lokacin, da kuma irin yadda taron makon hadin kan Musulmi da ake gudanarwa a gida (Nijeriya da makwaftanta) ya rika tasirin da har yakan sa ya kasa halartan taron Majma’ da ake gudanarwa duk shekara a Iran din.
Da yake bayanin Mauludin Manzon Rahma (S), Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana Manzon (S) da sakon da ya zo da shi a matsayin abu guda. Yace: “Manzon nan (S) shi aka aiko da sako. Kuma shi ba aikinsa ne kawai yace muku ga sakonku kawai ba. Ba ya zo ne ya samu mutane ya mika musu, yace musu ga sakonku (shikenan) ba. A’a, shi an rika saukar mashi da bayanin sakon ne a hankali a hankali har ya kammala. Ana saukarwa yana aikatawa, yana kuma koyar da mutane akan aikatawar, saboda haka shi ne alami na wannan sakon. Wato shi ne ‘ramzi’, da shi da sakon abu guda ne, abu daya ne.”
Yace: “Don haka ne ma a wajenmu, in mutum ya tauye darajar Annabi (S) ko da dan yaya ne, to a wurinmu ba ya tauye darajar addini da mikidarin wannan tauyewan ba ne (kawai), a’a, ya rusa addinin ne ma gabadaya.”
Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Da zaran an tauye darajar Annabi (S), to an rushe addinin ne. Don haka za ku ga makiya addinin gaskiyar magana, kullum sukan yi suka ne kan al’amarin Annabi (S), don in suka soki Annabi (sun san) suna rusa addinin ne”.
Ya kara da cewa: “Shi kan-kansa Manzon Allah (S) shi ma sakon ne, saboda haka shi ne aka ajiye a matsayin samfurin da za a kwafa. Wato ba za ka zama ka yi daidai da shi ba dama, amma za ka yi koyi da shi ne. Allah Ta’ala yana cewa: ‘Lakad kana lakum fi Rasulillahi uswatin hasanatun, liman kana yarjul Laha wak yaumal akhira….’ Kuna da kyakkyawan misali ga Manzon Allah (S), ga wanda yake kaunar Allah da ranar Lahira – shi ne Manzo ya zama abin koyi a gare ku.”
Jagora ya jaddada cewa, duk abinda ya shafi Manzon Allah, ko mene ne, to yana da daraja, don ya alamta Annabi (S) din ne. Don haka yace: “Muna iya cewa, ranar Mauludi ma yana daga cikin Sha’airullah”
Ya kawo fadin Sayyid Ibn Dawus da ke cewa: “Daidai gwargwadon murnarka a ranar haihuwar wani bawan Allah, daidai girman wannan bawan Allah din a wajenka.” Yace, idan aka ce ga fiyayyen halitta, shugaban Manzonni, shi kuma ana Mauludinsa (tuna ranar haihuwarsa), shi kuma ya kenan? “Kun ga ba za mu taba fifita wani kan Manzon Allah (S) ba, kuma ba za mu taba murnar da ya wuce wanda za mu yi a lokacin haihuwarsa ba.” Ya jaddada.
Jagora ya bukaci al’umma da su duba kawukansu su kwatanta da kammalallen sakon da Manzon Allah (S) ya zo ya isar a tsawon shekaru 23 na isar da sako. Yace: “Sakon nan da Manzon Allah (S) ya isar, ya kuma bar al’umma dore a kai, tambaya, a wane miqidari ne al’ummar nan take akan sakon? Ka dubi sakon da Annabi (S) ya zo da shi, ka kuma dubi al’ummar nan yadda take a yau. Sun yi daidai?”
A nan ne ya tunatar akan muhimmanci da wajabcin hadin kan Musulmi, da damuwa da al’amarin junansu, kamar yadda Manzon Allah (S) ya bar wasiyya. Ya kuma tunatar dangane da halin da al’ummar Palasdinu suke ciki, tare da kokawarsa akan halin ko in kula da duniyar Musulmi suke nunawa akan hakan. Sannan ya yi magana akan yadda makiya suke ta kokarin tarwatsa kasashen Musulmi, da kuma halin da aka jefa mu a Nijeriya na rigingimu daban-daban da sunan Kabilanci, ko da sunan bangaranci, ko da sunan addini.
Jagora (H) ya yi kira ga daliban akan su fahimci wazifar da ke kansu na cewa al’umma na jiransu a gida don su shayar da su tare da amfanar da su daga abin da suka samo na ilimi. Inda ya nuna babu bambanci tsakanin masu karatun Hauza da masu karatun Boko, dukkansu za su yi karatu ne na addini, wanda zai wa addini aiki. Yace: “Ku yanzu kun zo ne ku kamfata don ku je inda ake da kishin ruwansa… Kun zo ne ku dibi ilimi, sawa’un ko wane fanni kake karantawa, ko da ‘Engineering’ ne ko ‘Medicine’, in ka koma gida za ka yi ‘engineering’ da ‘medicine’ din addini ne.”
Ya bayyana cewa: “Da ace mutane sun bi koyarwar A’imma (AS) da shi kenan sun warke.” Yace: “Ban ce muku ba za a yi bincike (research) ba, to amma da ya yi sauki. Kawai nan da nan da mun fitar da ‘scientists’ wanda za su fitar mana da abubuwa daban-daban daga koyarwarsu. Alhamdulillahi ai an dan gwada a nan (Iran) an gani ko? Da aka dan kwama, aka yi tsokana, ai an gani ko?”
Shaikh Zakzaky (H) ya yi martani ga masu cewa cigaban fasahar Iran ba daga addini ba ne. Yace, su gane, lallai wannan ‘Technology’ din daga Allah ne. Domin cikin gajeren lokaci suka iya kai ga wannan matakin. “Ko ku yarda ko kar ku yarda, al’amarin Allah ne ke cikin (cigaban Iran), kuma shiriya ce ta Allah, kuma kadan ma kuka gani insha Allahul Azeem.”
Da yake bayan kammala jawabin Jagora (H), an bukaci ya dora rawani ga wasu ba’adin ‘yan uwa, sai ya zama mutum guda ne ya samu halartan muhallin a cikinsu, don haka bayan dora masa rawanin, Jagora (H) ya yi masa addu’a, sannan kuma ya ja hankali akan kiyaye daraja da alfarmar rawani.
Yace: “Da na ji kun yi magana dangane da rawani, nace to dama rawani ba sarauta ne ba fa, dawainiya ne. Wato ana nufin mutum ya alamta addini ne.”
Ya ce, ya kamata tunda shi an saka masa rawani, ya zama ramzi na abinda yake siffatawa. “Dazu ina magana akan cewa, Manzon Rahma (S) shi ne ramzi ‘perfect’ na addini. To kai kuma daidai gwargwado za ka zama ramzi ne na addini din, ta yadda za a ga addini a ‘suluk’ dinka, a zantukanka da ayyukanka, ta yadda ba za a ga wadansu ayyuka wanda suka saba ma addini ba.”
Jagora ya ja hankali akan kar sanya rawanin ya zama don ‘business’ kawai, ta yadda za a rika ajiye shi a lokutan rayuwa, sai in za a yi jawabi sannan a dauko a saka. “Ya zama ainihin in mutum ya sa rawanin nan, to yana nan a kansa ko ma ina ne za shi, don ya zama yana alamta abin (a dukkan rayuwarsa).”
A karshen Jawabinsa, Jagora ya yi fatan Allah Ya bayyanar da wanda da bayyanarsa ne za a samu mafita, karshen makiya ya zo, adalci ya tabbata, duk abubuwan nan su kwaranye, mu samu izzar da ba za mu ga irinta ba Insha Allah. “Muna fatan ya zama muna nan za a yi, don an kusa. In kuma Allah ya dauki ranmu kafin lokacin, Allah Ya dawo da mu a yi da mu, insha Allah.” Ya karkare.
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
11/September/2025




















Your Comment