A Gaza, ba a auna tazarar kilomita, ko cikin mintuna ko sa'o'i. Lokaci ya zama lokacin jira don mutuwa ko tsira na ɗan lokaci. Nisan da ke tsakanin gidanku da "wuri samun aminci" ya zama nisa tsakanin ku da mutuwa.
Shi kuwa kudi, gaba daya ya rasa ma’anarsa. Ko dala 2,000 a yau bazai saya maka inuwar tanti ba ko hayan filin da ba kowa don kare kai daga jahannamar tashin bom.
A cikin wannan dan karamin tsibiri, wanda yankinsa bai wuce murabba'in kilomita 365 ba, sama da mutane miliyan biyu ne ke rayuwa cikin wani mummunan mafarki da ya ci gaba da wanzuwa kusan shekaru biyu.
Kimanin shahidai 65,000, da wasu daruruwan dubbai da ne suka jikkata, ko suka bace, ko suka gudu matsugunansu, duk a cikin yakin kare dangi, da ke lalata rayuwa gaba daya.
Hijira Daga Gaza Zuwa "Yankin Mai Aminci"… Tafiya Zuwa Wurin Da Ba Dawowa
Tare da fara mamayar Isra'ila ta ayyana dukkan birnin Gaza a matsayin "yankin yaki mai hatsari," an bukaci mazauna yankin da su fice zuwa kudu zuwa yankin da ake kira "yankin aminci," duk da cewa harin bam din yana kaiwa har wadannan yankunan.
Amma sufuri a Gaza a yau ba kamar yadda yake ba. Kafin yakin, tafiya daga arewa mai nisa na Tiri zuwa kudu ta dauki sa'a guda kawai a mota.
Yanzu, irin wannan tafiya za ta iya komawa zuwa sa'o'i tara na jira, tsoro, neman mai, bude hanyoyi, da direban da zayyi kasada.
Mayada Muhanna, wata ’yar shekara 41 da ke da ‘ya’ya uku da yaki ya raba da muhallansu sau biyu a cikin shekaru biyu ta ce: “Ka yi tunanin yin tafiya daga unguwa zuwa unguwa, kamar kana tsallaka nahiyar gaba daya ba tare da tabbacin cewa za ka isa da rai ba.
Kaura Da Hijira Amma Gurin Zuwa
Mayada, wadda ta rasa gidanta da mahaifinta a lokacin yaƙin, ta kwatanta “kaurar ba tare da sanin wajen zuwa ba.” Ta ce, “A karo na farko, akwai wani abu mai kama da rayuwa, za mu iya hayan mota, mu sayi abinci, har ma mu sami wurin zama, a yau? Ba tanti, ba kasuwa, babu hanyoyi, babu fatan rayuwa”.
Mayada ta yi hayar babbar mota tare da ’yan uwanta a kan shekel 2,500 kacal don jigilar ‘yan kaya. "Na san iyalai da suka fito daga karkashin baraguzan gine-gine kuma ba su iya daukar bargo tare da su ba.
"Filin da babu kowa a cikinsa, ko da babu ruwa ko wutar lantarki, yana kashe dubunnan shekel. Abin na hauka ne. A wajen Gaza, muna taimakon junanmu, amma yawancin mutane ba sa samun ma wanda zai aika musu da burodi," in ji ta.
Mutuwa Ta Kowane Ɓangare
Suhail Abu al-Araj, mai shekaru 33, ya ci gaba da zama a Gaza duk da yakin saboda kawai "ba shi da wani zabi".
Ya ce, "Mutane sun ce ku fita...to zuwa ina? Duk wanda na sani ya yi shahada ko kuma ba zai iya daukar kowa ba, na rasa komai, har aikina da kudin shigata".
Abu Al-Araj, wanda ya rasa mahaifinsa saboda rashin maganin cututtuka masu tsanani, yanzu yana rayuwa cikin fatan tsira wata rana. "Kowace dare ina jin kamar shi ne na ƙarshe. Amma na ci gaba da ƙoƙari ... ba don ni ba, amma ga 'ya'yana mata, waɗanda lafiyarsu ta tabarbare kafin yakin".
Tanti Mafarki Ne Wanda Ba Zaka Iya Samunsa Ba
Dangane da hakan Muhammed Miqdad, mai shekaru 37, ya yi gudun hijira fiye da sau daya. Ya gina tanti a farkon yakin yana amfani da itace da leda nailan da ya saya a kasuwar Rafah.
"Ba tanti ba ne, waurin sanyi ne kawai," in ji shi. Da ya koma Gaza, ya tarar da wani sashe na gidansa a tsaye, ya zauna a can na dan lokaci kafin a sake tilasta masa barinsa. Yanzu, babu tanti, babu gida, bai kuma san inda zai kwana ba.
Mohammed ya kara da cewa "Ina tafiya tsakanin 'yan uwa da abokan arziki, ina neman wurin da zan iya gina tanti tun daga tushe, amma ko fili ya zama mafarki,".
Tsakanin kowane shahidi, da wanda ya rasa matsuguninsa, da wanda ba shi da matsuguni, akwai labarin da ba a taɓa ji ba, da ciwon da ba a rubuta ba, da kuma rayuwar da ta wargaje ba tare da kowa ya sani ba a ɗaya daga cikin wurare masu cunkoson jama'a da wahala a duniya.
Your Comment