12 Satumba 2025 - 22:35
Source: ABNA24
An Gudanar Da Bukukuwan Maulidin Manzon Allah (Saww) Da Iyalansa A Kasar Kamaru.

An gudanar da bikin Maulidin Manzon Allah SAW a Jamhuriyar Kamaru, inda aka gabatar da lacca mai taken falalar Manzon Allah SAW da alayensa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sashen ilimi da al'adu na Atbatul-Abbasiyya (a.S) ya shirya wani biki na tunawa da maulidin manzon Allah mai tsira da amincin Allah a Jamhuriyar Kamaru.

Sheikh Muhammad Mukhtar babban jami’in cibiyar nazarin nahiyar Afirka a kasar Kamaru ya bayyana cewa: “Cibiyar ta gudanar da bukukuwan murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a kauyen Kombo da ke Jamhuriyar Kamaru.

Ya kara da cewa: “Bikin ya hada da lakcoci na addini kan falalar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), da rayuwarsa mai albarka, da tasirinsu wajen shiryar da bil’adama da yada dabi’u na rahama, da adalci, da soyayya.

Wannan biki na daga cikin jerin ayyuka da cibiyar ta gudanar a kasashen Afirka da dama, da nufin farfado da ambaton Manzon Allah da alayensa (amincin Allah ya tabbata a gare su), da kuma kara wayar da kan al'umma kan rayuwarsu da kuma manyan darussa da suke tare da su.

Your Comment

You are replying to: .
captcha