13 Satumba 2025 - 08:35
Source: ABNA24
Falasdinawa 70 Su Kai Shahada A Safiyar Yau A Gaza

Falasdinawa 70 ne suka yi shahada tun a safiyar yau (Asabar) sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a yankunan Sheikh Radwan da Jabalia Nuzla a Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hare-hare sama da 18 kan makarantu da matsugunan gaggawa da kuma gidajen zama da bankin Quds a birnin Gaza a safiyar yau Asabar.

Your Comment

You are replying to: .
captcha