4 Faburairu 2026 - 22:40
Source: ABNA24
An Gudanar Da Taron Nisf-Sha'aban 1447 A Abuja Najeriya + Hotuna

Da yammacin Talata 15 ga Sha'aban 1447 (3/2/2026) Harkar Musulunci a karkashin a karkashin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta gudanar da bikin Nisfu Sha'aban, don murna da zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (AS) a garin Abuja.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A yayin jawabinsa ga dimbin mahalarta, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana Imam Mahdi (AS) a matsayin macecin raunanan duniya, wanda yace, shi ne yake gudanar da al'amuranmu a yanzu haka.

“Mu fa ba muna jiran Imam Mahdi (AS) ya bayyana ba ne mu bi shi. Mu yanzu haka shi muke bi, shi ne shugabanmu, shi yake gudanar da alamarinmu.

Jagora ya bayyana yadda duniya ta dare biyu a sarari a wannan lokacin, yace: “Duniya tana darewa biyu ne, dama ta dare biyu tuntuni, amma ba kowa ne ya gane ba, amma yanzu an fara ganin darewan yana bayyana, da ma'abota dama da ma'abota hagu.”

Yace: “Idan aka dare, muminai a nan, kafirai a nan, to munafukai ina za su je?” Inda ya amsa da cewa: “Za su je wajen kafirai ne.”

Jagora (H) ya bayyana cewa, la-muhalata ƙwamawan nan sai an yi (a tsakanin ma'abota shiriya da ma'abota ɓata), sai fa an yi, sai an yi fa.”

Yace, yanzu makiya sun nuna suna da karfi, amma cikin ikon Allah, an nuna musu akwai karfin da ta fi tasu. “Lamuhalata, In ba su kai hari yanzu ba, za su kai hari nan gaba.... Kuma karshen su kenan.” Ya yi albishir.

Shaikh Zakzaky ya bayyana cigaba 'technology' din nan da sunan Allah da ake samu (musamman a Jamhuriyar Musulunci ta Iran), a matsayin wani koyarwa ne da shi Sahibul Asr ke bamu.

Yace, ba zai yiwu Allah Ta'ala Ya bar ƙasa wawai ba. Inda ya tabbatar da cewa, ba kamar yadda wasu mutane ke cewa Musulmi ba su da shugaba ba, mu muna da shugaba. “Ku ne baku da shugaba, mu muna da shugaba.”

Ya kara da cewa: “Al'ummar Musulmi suna da shugaba, sai dai wasu ne basu san shi ba.”

Shaikh Zakzaky ya jaddada cewa, Imam Mahdi (AS) ne shugabanmu da muke jiran bayyanarsa kurkusa. Yace: “Muna fatan bayyanar Sahibul Asr waz Zaman ya zama kwanan nan ne.”

Ya jaddada yadda duniya ke darewa gida biyu a wannan lokacin, tsakanin dakarun shiriya da na ɓata. Yace, azzalumai mahukunta na hujumi ga masu addini da barazana. “Suna cewa, za su ƙwace ƙasar ne. Za mu kwacen!!! Ba ku isa ku hana ba. Alƙawari ne na Allah. Ba ku isa ku hana ba. Barazanarku ta banza da hofi.”

Yace, “Kullum tsoronsu kar addini ya ɗago. Ba za mu hana ku ku yi tunanin ba. Sai dai mu yi muku albashir da karshenku na nan tafe.”

A ƙarshen jawabin nasa, Jagora (H) ya yi fatan, Allah Ta'ala Ya sa mu zama cikin dakarun Imam Mahdi (AS).

15/Sha’aban/1447

03/02/2026

Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Your Comment

You are replying to: .
captcha