Shaikh Zakzaky ya bayyana yadda koyaushe makiya suke ma ‘yan uwa masu gwagwarmayar yunkurin tabbatar da addini barazana da kisa da sunan ba su tsoro. Yace: “Har ma nakan fadi wata magana, na ma fadi wannan a ranar wata Yaumu Shuhada. Nace, to kun ga harbin nan (da suke yi mana), suna so su ba sauran mutane ne tsoro akan kada su shigo cikinmu, domin mu kashe mu ake yi. To ni ma zan ba da tsoron! Kun ga kashe mu ake yi ko? To, duk wanda ba ya son a kashe shi, kada ya shigo cikinmu!”
Jagora ya jaddada cewa, hatta ma wadanda suke tare da mu, amma suke jin tsoron kada a kashe su, to su tafi abinsu. “Duk wanda yake jin tsoron za a kashe shi (a cikinmu), to ya tafi abinsa, nan ba wurinsa ba ne. Nan muhallin wadanda suka ce, mun ba da ranmu ne.”
Yace; “(Mu) ba ‘yan-gamu-kashemu da ake cewa ba ne, ‘yan-gamu-kashemu ai bashi da ma’ana. A’a mun tsaya kyam a tafarkin Allah, ko da za a kashe mu. Shi ne abin nufi. Don haka, idan mutum yana jin tsoro, ya ba da wuri, ba muhallinsa ba ne nan.”
Ya cigaba da cewa: “Kuma mu da yake muhallin namu ne, to kuma wani ya yi kadan ya bamu tsoro. Da me za ka bamu tsoro? Harbi ne. To ka zo ka yi mana! Bismillah! Ba ma ka yi a da ba?” Yace: “Da ma ace ba ka yi ba ne, da sai mu ji tsoro. To ka riga ka yi. Me ya rage mana? Muna son mu ma mu tafi inda wadannan ‘yan uwan namu suka tafi ne, burinmu kenan.”
Shaikh Zakzaky ya tabbatar wa da azzalumai cewa, ba su da wani sauran abin yi mana barzana baya ga harbi da kisa, kuma ya riga ya zama baa bin tsoro a garemu ba. “Kun sa bindiga kun yi harbi. Iyakanta dai kenan ko? To da me kuma za ku bamu tsoro?”
Yace: “Za ka ba da tsoro ne da abinda ke bayar da tsoro, amma kar ka bari a gano wallenka (a wannan abin). Idan kuka yi harbi (yanzu), za a gano wallenku kenan. Ballantana irin wadanda kuka yi musu irin wannan kashe-kashen, su iyalan wadanda kuka yi ma kashe-kashe din, sam ba za su taba jin tsoronku ba. In ma wani ya ji tsoro, to banda su.”
Jagora wanda ya bayyana ma’anar nasara da cewa, ita ce tsaya kyam akan tafarki har mutum ya riski dayan biyu; ajali ko shahada a tafarkin Allah, ya tabbatar da cewa, ana samun nasara ne ta hanyar dakewa, kuma sakamakon dakewar ne zai sa azzalumai ba za su taba yin nasara akanmu ba.
Yace: “In mutum ya dake, har mutuwar ta same shi, shikenan Falillahil-hamd, ya cika a tafarki. Idan kuma ya zama shi ne sanadiyyar cikawansa, duk lafiya lau. Kowanne duka daidai ne, ‘imman-nasru awish-shahada ne’, dukansu kuma ‘ihidal-husnayain’ ne, - wato dayan biyu kyawawa ne; nasara ko shahada.”
“To nasarar nan kamar abinda ake ce ma alakoro ne, - wani abinda za a dan baka kafin cikakken. “Ukra tuhibbunahaa, nasrun minallahi wa fatahun Qareeb, wa basshiril Muminin” Wani abu ne dan kadan wanda bai kai wancan ba, kafin wancan. “Nasrun minallahi wa fatahun Qareeb” a nan, can kuma insha Allahu “Jannatin Tajriy min tahtihal anharu khalidina fiyha.” Kaga da me mutum ya manta?” Jagora ya nanata.
Don haka ya jaddada kira ga iyalan Shahidai da cewa: “Su ‘ya’yan Shahidai, ya kamata su tsaya ne kyam akan cewa, su fa kam sai sun ba mara da kunya. Sai sun nuna su kam jinainan iyayensu bai tafi a kawai ba. Ya zama sun dake daram a wannan tafarkin, har izuwa karewan ajali, ko su ma su yi Shahada su cimmusu, dayan biyu ne insha Allahu.”
A karshe, Jagora ya yi musu nasiha akan cigaba da da’awa ta hanyar kyawawan ayyuka, da tsayawa kyam a tafarki wanda ke bukatar ilimi da aiki da ilimin, da mujahada; ibada, sallah da kula da Ma’asurat, da kuma kiyaye tsafta, da biyayya, da kyakkyawan hali, har ya zama shakhsiyyan addini ya zama ya ginu a tare da su, ta yadda in an gansu an ga addini, in suka yi magana za a ji addini, in suka yi aiki a ga addini, in aka yi hulda da su za a ga addini. “Ka zama alamin addini a duk abinda kake yi. Wannan shi ne zai kai mu ga nasara, duniyarmu da lahirarmu.”
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
01/12/2025
Your Comment