5 Satumba 2025 - 12:59
Source: ABNA24
Yemen: Miliyoyin Mutane Ne Duka Halarci Maulidin Annabi Muhammad (Sawa)

Miliyoyin Mutane yamanawa ne suka Halarci Maulidin Annabi Muhammad A Sana'a

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: An fitar da hotunan farko na yadda miliyoyin al'ummar kasar Yemen suka halarci bukukuwan maulidin Manzon Allah (SAW) a ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal shekara ta 1447 bayan hijira a dandalin Sab'een a birnin Sanaa.

Babban taron wanda aka gudanar da taken ''Hashdur Rabi'il Muhammadi'' ya cika da mahalarta sanye da korayen huluna da korayen tutoci tare da lullube kasar Yemen da korayen tutoci da banoni.

Ta hanyar daga babbar tutar Falasdinu, al'ummar sun nuna goyon bayansu ga al'ummar wannan kasa da ake zalunta da kuma tsananin kaunarsu ga matsayi mai tsarki na Annabi Muhammad (SAW).

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha