-
Labarai Cikin Hotuna Na Zaman Makoki A Kwanakin Karshe Na Safar A Kabul
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarto maku cewa: an gudanar da zaman makokin wafatin manzon Allah (SAW) da shahadar Imam Hasan Mujtabi da Imam Rida As, bisa daukar nauyin cibiyar (Huriyyatul Insiyya) A cikin Babbar Husainiya da ke ganuwar Fathullah a Kabul.
-
Falasdinawa 48 Sun Yi Shahada A Gaza / Adadin Shahidai Ya Kai 40,786
Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a zirin Gaza ta sanar a cikin wata sanarwa a rana ta 332 na yakin cewa sojojin yahudawan sahyoniya sun sake yin kisan kiyashi har sau 3 kan fararen hula Palasdinawa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
-
Ansarullah: Hare-haren Da Makiya Suka Aikata Na Baya-bayan Nan Su Ne ne Farmaki Mafi Girma Na Yunkurin Ƙauracewar Falasdinawa Daga Gidajensu Cikin Shekaru 20 Da Suka Gabata
Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta sanar da cewa hare-haren da Isra'ila ta kai a baya-bayan nan a yammacin gabar kogin Jordan da nufin samar da tsoro da fargabar fararen hula shi ne farmaki mafi girman muni a cikin shekaru 20 da suka gabata.
-
Aci Gaba Da Kai Hare-Hare A Yammacin Gabar Kogin Jordan Sojojin Yahudawan Sahyoniya 2 Sun Mutu
Kafofin yada labaran gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun sanar da afkuwar wani farmaki da masu kin jinin Sahyoniyawa suka kai a arewacin birnin Hebron da ke gabar yammacin gabar kogin Jordan, inda aka ce ya zuwa yanzu mutane biyu suka mutu.
-
Ayyukan Ta'addanci Na Kara Karuwa A Sansanin 'Yan Gudun Hijirar Myanmar; Daga Kashe Musulmi Da Jirgi Mara Matuki Zuwa Sace Yara Maza Domin Yaki
Wasu gungun 'yan awaren Myanmar sun kashe wani adadi mai yawa na Musulman Rohingya inda suka kai hari da jiragen yaki marasa matuki Akansu.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na gudanar da gagarumin tattaki na makokin Arbaeen a birnin Istanbul kasar Turkiyya
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku cewa: dubun dubatar mabiya mazhabar shi'a na kasar Turkiyya ne suka hallara a ranar Arbaeen domin gudanar da tattakin makokin Arbaeen din shahadar Imam Husain (AS) a yankin "Halkali" da ke birnin Istanbul. .
-
A farko dai shi Imam Husain mutum ne wanda ya san ‘Yan Adamtaka
Yanzu abunda ya ke faruwa a Gaza ya isa al’ummar musulmin duniya kuka da takaici domin kowane lokaci ana kashe ‘yan uwanmu kamar kiyashi a gurin
-
Yahudawa Na Shirin Gina Majami'an A Cikin Masallacin Qudus
Ben Gweir yana neman gina majami'a a cikin Masallacin Al-Aqsa inda ya sha suka akan maganganunsa
-
Cikakken Jawabin Sayyid Hasan Nasrallah Dangane Harin Maida Martani Da Kungiyar Hisbulla Ta Fara Yau Akan Is’raila Bisa Kashe Kwamandanta Da Ta Yi.
Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, yayi bayani sa'o'i kadan bayan fara gagarumin martani na farko na kungiyar dangane da ramuwa ga ayyukan ta'addancin da gwamnatin sahyoniyawan sahyoniya ta yi a baya-bayan nan a shahadantar da Fu’ad Shukri, daya daga cikin kwamandojin gwagwarmaya a yankunan kudancin birnin Beirut.
-
Ansarullah: Za Mu Sumbaci Hannayen Jaruman Hizbullah Don Jinjina Masu /Martanin Yaman Na Kan Hanya.
A wannan mataki na mayar da martani, Hizbullah ta kai hari kan sansanoni 11 da wuraren soji na gwamnatin sahyoniyawan.
-
Hizbullah: Mun Yaudare Sojojin Isra'ila Da Makami mai linzami/Mun Kai Hari Muhimman Wurare 2 A Tel Aviv
Hizbullah tace sun yaudari sojojin Isra'ila da makamai masu linzami inda suka kai hari a muhimman wurare guda biyu a Tel Aviv
-
Shaikh Al-Zakzaky: Masu Goyon Bayan Falasdinu Sun Fito Ne Daga Makarantar Imam Husaini As
A wajen rufe Maukibin kiran Al-Aqsa da aka gudanar a kan hanyar masu ziyara a Karbala mai alfarma, Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: Duk da irin goyon bayan da mamaya ke samu daga manyan kasashen duniya, ya zuwa yanzu ba ta iya yin komai ba illa kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Bisa la'akari da cewa Palasdinawa na fuskantar girman kan duniya baki daya.
-
Hizbullah Ta Kai Harin makami mai linzami kan sansanin "Maroon".
Majiyar Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah ta kai hari kan wani sansanin sojin sama na gwamnatin sahyoniyawan da manyan makamai masu linzami a arewacin Palastinu da ta mamaye.
-
Adadin Shahidan Falasdinawa Ya Karu Zuwa Mutane 40,223
Adadin shahidai a Gaza ya kai 40,223 sakamakon ci gaba da hare-haren wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawan ya haifar da kara samun shahadar wasu Falasdinawa 50.
-
Hizbullah Ta Tayi Ruwan Rokoki A Yankin Golan | Yahudawa Sun Martani Ga Ministan Tsaro Da Cewa: Barka Da Safiya! + Bidiyo.
Hizbullah Takai Harin Makami Mai Linzami Da Jiragen Sama Maras Matuki Kan Arewacin Falasdinu Da Aka Mamaye Da Yankin Golan Na Kasar Syria + Bidiyo.
Jaridar yahudawan sahyoniya ta Yediot Aharnot ta bayyana hare-haren na yau da kungiyar Hizbullah ta kai a kasar Labanon a matsayin mai hadari da ba a taba ganin irinsa ba.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Ganawar Sheikh Ibrahim Ya'aqub AlzakzakyDa Shaikh Ahmad Safi
Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA- ya habarta maku cewa: Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky(H) ya gana tare da Shaikh Ahmad Safi (shugaban ɓangaren addini na Ataba Husainiyyah) da Shaikh Ahmad Amuli (shugaban makarantun Addini ƙarƙashin Ataba Husainiyyah) tare da wasu ba'adin Malamai na ƙasar Iraqi.
-
Jami'an Tsaron Isra'ila Cikin Damuwa Da Aukuwar Wata Sabuwar Intifada A Gabar Yammacin Kogin Jordan Bayan Harin Tel Aviv
Jaridar ‘Yediot Aharnot’ ta yahudawan sahyuniya ta ruwaito damuwar jami’an tsaro na gwamnatin sahyoniyawa game da faruwar wani sabon intifada a yammacin gabar kogin Jordan tare da daukar matakin yaki da yahudawan sahyoniya a birnin Tel Aviv na baya-bayan nan a matsayin daya daga cikin alamominsa.
-
Hizbullah Ta Kai Harin Makami Mai Linzami Kan Falasdinu Da Aka Mamaye
Gwamnatin Sahayoniya ta sanar da kai wani kazamin hari da makamin roka da kungiyar Hizbullah ta kai kan yankunan arewacin Palastinu da ta mamaye da suka hada da Gabar Galili da Tuddan Golan.
-
Labarai Cikin Hotuna An Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Mai Taken "Sakon Karbala" A Birnin Calcutta Na Kasar Indiya
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku cewa tare da halartar gungun mabiya mazhabar shi'a, an gudanar da wani gagarumin taron karawa juna sani kan batun Karbala mai taken "Sakon Karbala" a birnin Calcutta na kasar Indiya, inda a cikin wannan taron mabiya addinai da dama sun halarta.
-
Alkaluma Masu Ban Tsoro Daga Yakin Gaza; Mutane 10,000 Ne Suka Bace Sannan Kuma Gawarwakin Shahidai 1,760 Suka Kone
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Falasdinu ta fitar da alkaluman da ba a taba jin irinsu ba na bala'in yakin da yake samun mutane a Gaza bayan watanni 11 tun farkon fara fitar da adadin rayukan da yakin ya shafa, wanda ke nuni da cewa mutane 10,000 ne suka rage a karkashin baraguzan gine-gine da kuma gawarwakin shahidai kusan 1,760 da suka kone, duka wadannan rayuka sun salwanta ne saboda anfanin da makaman da aka haramta da gwamnatin Sahayoniya ta yi akansu.
-
Blinken A Ganawarsa Da Shugaban Gwamnatin Sahyoniyawa: Tattaunawar Gaza Na Iya Zama Dama Ta Karshe Don Cimma Yarjejeniya.
Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, wanda ya ziyarci yankunan Falasdinawa da aka mamaye, ya gana da shugaban kasar Isra'ila Is’haq Herzog a yau (Litinin) inda ya ce tattaunawar da ake yi dangane da Gaza na iya zama "dama ta karshe" na cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin.
-
Jiragen Yakin Isra’ila Sun Jajjefa Bama-Bamai Masu Yawa A Kudancin Gaza
Harin da aka kai kan gidajen Falasdinawa a gabashin Khan Yunus ya yi sanadiyyar shahidai akalla hudu da jikkata shida.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Zanga-Zangar Al'ummar Koriya Ta Kudu Domin Yin Allah Wadai Da Kisan Kiyashin Da Yahudawan Sahyuniya Suka Yi A Gaza
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku cewa: al'ummar kasar Koriya ta Kudu da suka shafe makonni suna shirye-shiryen gudanar da zanga-zangar kin jinin haramtacciyar kasar Isra'ila, sun gudanar da zanga-zanga a yau ranar 15 ga watan Agustan (25 ga watan Murdad) domin nuna kin jininsu ga laifukan da gwamnatin sahyoniyawan ta ke yi wa mutanen Gaza da ake zalunta.
-
Bayyanar Alamun Rugujewar Gwamnatin Sahayoniya/ Shan Kayensu Wajen Gudanar Da Yaƙi Na Gajeren Lokaci "Ben-Gurion" + Bidiyo
Fasikanci da dabbancin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila yana kara fitowa fili yayin suke hana shigowar magunguna, abinci, da duk wani taimako ga rayuwar al'ummar zirin Gaza, kuma wannan tsari yana haifar da bayyanar cututtuka daban-daban, da yaduwar yunwa da sauran tabarbarewar rayuwar mutane.
-
Falasdinawa 12 Ne Suka Yi Shahada A Harin Da Yahudawan Sahyuniya Suka Kai A Khan Yunis
Majiyoyin labarai sun ba da rahoton ci gaba da kai hare-hare da gwamnatin sahyoniyawan ke kai wa zirin Gaza da kuma shahadantar da Palastinawa 12 a lokacin da sojojin wannan gwamnati suka kai harin a "Khan Yunis" da ke kudancin wannan waje.
-
Labarai Cikin Hotuna Na Yadda Yaran Suke Yiwa Maziyarta Imam Hussain (A.S.) Hidima.
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya kawo maku rahoton cewa: Taron Arbaeen na Imam Husaini (As) na daya daga cikin manya-manyan taruka masu kayatarwa da ban sha'awa na addini wanda a ko da yaushe ake baje kolin kyawawan siffofi da halaye na sadaukar da kai da tausayawa da ikhlasi da imani.
-
Rahoto Cikin Hotuna Na Gudanar Da Zaman Makokin Shahadar Sayyida Ruqiyyah (A.S) A Masallacin Kufa
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya kawo maku rahoton cewa:, an gudanar da zaman makoki na daren shahadar Sayyida Ruqayyah a masallacin Kufa da ke Iraki, tare da halartar dimbin mabiya mazhabar Ahlul Baiti (a.s).
-
Mummunan Harin Kare Dangin Da Yahudawan Sahyoniya Suka Aikata A Gaza A Yau; Sama Da Mutane 100 Ne Suka Yi Shahada + Hotuna
Dakarun gwamnatin sahyoniyawan sun sake yin wani aika-aikar ta’addanci a Gaza a safiyar yau Asabar, inda mutane da dama kusan 150 suka yi shahada tare da jikkatar wasu.
-
An Aika Sakon Barazana Ga Dubunnan Sahyoniyawan: Za A Binne Ku Mako Mai Zuwa
Majiyoyin labarai sun bayar da rahoton aike da sakonnin barazana ga wayoyin salula na dubban yahudawan sahyoniyawan da ke yankunan da aka mamaye.
-
Bidiyon Mummunan Harin Da Gwamnatin Sahayoniya Ta Kai A Gaza Da Safiyar Yau
Falasdinawa Sama Da 100 Su Kai Shahada Yayin Da Suke Sallar Asubah A Wani Harin Sama Da Isra’ila Ta Kai A Wata Makaranta A Gaza + Bidiyo
Majiyoyin labarai a safiyar yau Asabar sun bayar da rahoton shahadar Falasdinawa sama da 100 a harin da Isra’ila ta kai kan wata makaranta a birnin Gaza.