25 Agusta 2024 - 17:34
Ansarullah: Za Mu Sumbaci Hannayen Jaruman Hizbullah Don Jinjina Masu /Martanin Yaman Na Kan Hanya.

A wannan mataki na mayar da martani, Hizbullah ta kai hari kan sansanoni 11 da wuraren soji na gwamnatin sahyoniyawan.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti As Abna ya habarto maku cewa tashar -IRNA- ta hakaito cewa A cikin wata sanarwa da kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta fitar a lokacin da take taya kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon murnar harin martanin da takai na kashe babban kwamandan Jihadi Fu'ad Shukri, ta jaddada cewa martanin da sojojin Yaman zasu kai kan hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawa a birnin Hudaidah yana kan hanya.

Kamfanin dillancin labarai na IRNA na kasar Iran ya habarta bisa nakaltowa daga tashar Al-Masirah cewa, ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya sanar a cikin wata sanarwa cewa: Muna taya kungiyar Hizbullah da babban sakatarenta murnar wannan gagarumin hari na jarumta da suka kai kan makiya haramtacciyar kasar Isra'ila a safiyar yau.

An bayyana a cikin wannan sanarwa cewa: Wannan martani mai karfi da inganci a cikin zurfin tushen mamaya yana tabbatar da iko da karfi na hakikar gwagwarmaya na alkawura da barazana.

Ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ya ci gaba da cewa: Muna masu musabaha da hannaye na jaruman gwagwarmayar muslunci na kasar Labanon tare da goyon bayan duk wani zabi da aiki da za a yi don mayar da martani ga makiya yahudawan sahyoniya.

Harkar Ansarullah ta ci gaba da bayanin cewa: Muna sake jaddada cewa martanin kasar Yaman (ga harin da gwamnatin sahyoniyawan ta kai a kan Hudaidah) yana nan tafe, kuma ranaku da darare da fagage ne zasu tabbatar da hakan.

Wannan sanarwa ta fito ne bayan da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar a safiyar yau cewa ta kammala matakin farko na mayar da martani kan kisan kwamandanta na jihadi Fu'ad Shukri.

A wannan mataki na mayar da martani, Hizbullah ta kai hari kan sansanoni 11 da wuraren soji na gwamnatin sahyoniyawan.

Majiyar kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa: Sojojin Isra'ila sun gaza dakile harin da jiragen da muka kai musu marasa matuka, inda muka yi nasarar kawar da hankulan sojojin Isra'ila ta hanyar harba makamai masu linzami.

Ta kuma sanar da cewa: Mun kai hari kan manyan wurare guda biyu a arewacin Tel Aviv, wadanda za mu sanar nan gaba.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya gabatar da jawabi kan wannan aiki da misalin karfe 18:00 agogon Beirut (18:30 agogon Tehran).