Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta
maku cewa: kusan watanni 10 ke nan da hare-haren guguwar Al-Aqsa a ranar
7 ga watan Oktoban 2023, kuma ana daukar wannan yakin a matsayin daya daga
cikin mafi dadewa na yakin gwamnatin sahyoniyawan a kan Mutanen Falasdinawa marasa
tsaro a tsawon tarihi. Yakin da ya jefa Palasdinawa musamman al'ummar Zirin
Gaza cikin wani yanayi mai matukar tabarbarewa na tsawon watanni a jere, har
sai da akasarin al'ummar duniya musamman mazauna kasashen Turai suka tashi don
nuna goyon bayansu ga wadannan mutane tare da nuna rashin amincewarsu da adawarsu
ga manufofin kin jinin dan Adam na majalisar ministocin Netanyahu; To sai dai
wannan tsari ba zai iya samar da wani shinge ga kisan gilla da yahudawan
sahyoniya suke yi wa mazauna yankin zirin Gaza tare da goyon bayan Amurka kai
tsaye ba.
Shan Kayen Ga Manufofin Yakin Gajeren Lokaci Na Ben-Gurion
A tsawon shekaru saba'in da biyar na mamayar yankunan Palastinawa da yahudawan sahyuniya suka yi, wannan shi ne karo na farko da aka tsawaita yakin da ake yi tsakanin Yahudawa da Larabawa tsawon watanni a jere, yayin da daya daga cikin manyan kuma muhimman ka'idoji na wanda ya kafa gwamnatin Sahayoniya (David Ben-Gurion) shi ne "sauri da gajartar yakin da rashin wargajewar sa" inda kuma suke dauki tsawaita yakin a matsayin dalili na gazawa da koma bayan wannan gwamnatin.
Dangane da haka, manazarta da masana harkokin soji na gwamnatin sahyoniyawan da dama sun yarda cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suna fada ne ba tare da wata manufa ba, kuma ba su da iko juya yakin da ake yi a zirin Gaza. Sun yi imanin cewa galibin yankunan Zirin Gaza ba sa dauke da 'yan ta'addar yahudawan sahyoniya kuma ba a lura tare da la’akari da kasancewarsu a fili ba.
Kafin nan; Ana kuma jin labarin farfado da karfafawa da kuma maido da tsarin kungiyar soji ta Hamas, wanda ake ganin tamkar karyatawa ce ta ikirari da yahudawan sahyuniya suka yi na rusa wannan kungiyar ta soja. A hakikanin gaskiya babbar nasarar kungiyar Hamas da shan kayen sahyoniyawan ya faru ne; saboda shigar da sojojin Isra'ila suka yi a yakin da basu san zurfinsa ba (yakin da ba a tsari yak e ba) da kungiyar gwagwarmayar Hamas. Ta hanyar amfani da wannan dabarar yaki, sun yi nasarar rage karfin iko da ingancin sojojin Isra'ila zuwa mafi kankantar abin da zai yiwu tare da alakanta wannan gwamnatin ta kwace da rikicin siyasa da na soja da ba a taba gani ba.
Gazawar Gwamnatin Sahyoniyawan Wajen Tinkarar Farmakin Guguwar Al-Aqsa
A yau, a bayyane yake ga kowa cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas da mutanen da ke zaune a zirin Gaza su kadai ne a farkon farmakin guguwar Al-Aqsa saboda dalilai na tsaro. Amma nan da nan bayan fara farmakin da bayyanar shi; Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da sojojin Yaman da sauran kasashen da ke goyon bayan Falasdinu sun shiga wannan yakin kuma sun samu nasarori da dama har zuwa abunda ya kawo yau, wanda hakan ke nuna gazawar sojojin yahudawan sahyoniya wajen tunkarar su. Watau; Yanzu Tel Aviv tana sane da cewa daidaiton soji da ke tsakanin sojojin Isra'ila da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas da magoya bayanta bai bada damar kawo karshen yakin ba, kuma wannan yaki ya dauki wani tsari na gazawa a cikin watannin da suka gabata, kuma Sakamakon ba komai bane illa badakalar soja da rugujewar karfin karya na wannan gwamantin .
Dangane da haka, ya kamata a lura cewa, duk da abin da aka watsa a kowane nau'in watsa labarai na gani da sauti na duniya; Sojojin gwamnatin yahudawan sahyoniya ba su da karfin gwiwa da da jarumta wajen gudanar da cikakken yaki, kuma wannan tsari ya dogara ne da abubuwa da dama da suka hada da daidaiton karfin soja, gami da karuwar bambance-bambance masu yawa tsakanin manyan siyasa da sojojin jami'an gwamnatin Isra'ila. Tsarin rikicin da babu shakka ba za a iya magance shi cikin kankanin lokaci ba kuma ya samar da hujjar tabbatar da gazawar majalisar ministocin Netanyahu a duniya.
Sojojin Gwamnatin Sahayoniya Sun Kasance Mafi Girman Munin Halaye A Duniya
Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar a zirin Gaza; Ya zuwa yanzu sama da mutane dubu 39 da 583 ne suka yi shahada a wannan yakin sannan mutane dubu 91 da 398 suka jikkata, sannan dubban mutane sun bace, lamarin da ya sa wannan yakin ba a taba ganin irinsa ba. Yakin da a cewar Sayyid Hasan Nasrallah (Sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon) sojojin yahudawan sahyuniya a matsayin sojojin da suka fi fasikanci a duniya.
Fasikanci da zaluncin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila yana kara fitowa fili yayin da ya kasance hana shigowa da magunguna, abinci da duk wani taimako na rayuwar al'ummar Gaza na daga cikin ajandarsu, kuma wannan tsari yana haifar da bayyanar cututtuka daban-daban, da yaduwar yunwa da sauran tabarbarewa yanayin rayuwar mutane; Don haka ya zama wajibi ga kowane musulmi ya tashi tsaye ya yi wani abu na taimakon al'ummar Gaza. Domin fuskantar azzalumai da kare wanda ake zalunta da rashin mika kai cikin kaskanci su ne abubuwan da Imam Husaini (a.s) ya sanya a gaba, wanda ya kasance fitilar rayuwa ga musulmi a tsawon tarihi.
Ƙarshe Zamu Iya Kaiwa Ga Sakamo Kamar Haka:
Bayan fiye da kwanaki 300 na yaki a zirin Gaza; Babu daya daga cikin manufofin gwamnatin yahudawan sahyoniya da ta cimmawa, kuma wannan yaki bai haifar da wani sakamako ba face tabarbarewar ikon da wannan hukuma take da shi da kuma bayyanar da sabanin siyasa a tsakanin manyan jami'anta. Za a iya cewa wannan yaki shi ne yaki mafi tsawo a tarihin mamayar Falasdinu, wanda ya janyo wa gwamnatin sahyoniyawan fada cikin rikicin da ba a taba ganin irinsa ba, da matsaloli masu dimbin yawa, wanda ya sa duniya ta yi zanga-zanga da tinkarar gwamnatin Netanyahu, kuma a kan wannan tafarkin; An samar da shimfidar da tushe na rugujewa da gushewar gwamnatin Sahayoniya.
