31 Agusta 2024 - 09:10
Ayyukan Ta'addanci Na Kara Karuwa A Sansanin 'Yan Gudun Hijirar Myanmar; Daga Kashe Musulmi Da Jirgi Mara Matuki Zuwa Sace Yara Maza Domin Yaki

Wasu gungun 'yan awaren Myanmar sun kashe wani adadi mai yawa na Musulman Rohingya inda suka kai hari da jiragen yaki marasa matuki Akansu.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya kawo maku rahoton cewa: tashar CNN ta sanar a cikin wani rahoto da ta fitar cewa, an kashe wani adadi mai yawa na Musulman Rohingya sakamakon hare-haren da wata kungiyar 'yan awaren Myanmar ta kai.

Rahoton ya ce fargabar kisan kabilanci a kan al'ummar musulmin Rohingya ya sake kunno kai bayan da aka kashe daruruwan mutane da suka hada da mata da kananan yara da suka tsere daga jihar Rakhine da ke yammacin kasar Myanmar.

Hotunan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta ta hanyar CNN sun nuna gawarwaki da dama da suka zube a bakin kogin Naf, wanda ya raba Myanmar da Bangladesh.

Shaidu da masu fafutuka na Rohingya sun shaida wa CNN cewa, wasu jerin hare-haren jiragen sama a ranar 5 ga watan Agusta sun auna fararen hula da ke gujewa fada da tashe-tashen hankula a kauyukansu da ke arewacin Rakhine.

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce adadin wadanda suka mutu ya haura 200, wanda idan har aka tabbatar da hakan zai kasance daya daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai kan fararen hula a yakin basasar Myanmar na shekaru uku.

A lokaci guda; Sace matasa maza da samari 'yan Rohingya da ke zaune a sansanonin; Wani sabon damuwa ne wanda ya firgita iyalai da dama da abun ya shafa.

A cewar rahotanni; Ya zuwa yanzu, yara maza da yawa sun bace daga sansanonin 'yan gudun hijira.