1 Satumba 2024 - 05:54
Aci Gaba Da Kai Hare-Hare A Yammacin Gabar Kogin Jordan Sojojin Yahudawan Sahyoniya 2 Sun Mutu

Kafofin yada labaran gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun sanar da afkuwar wani farmaki da masu kin jinin Sahyoniyawa suka kai a arewacin birnin Hebron da ke gabar yammacin gabar kogin Jordan, inda aka ce ya zuwa yanzu mutane biyu suka mutu.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku cewa, a safiyar yau Lahadi ne kafofin yada labaran gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bayar da rahoton afkuwar wani hari da masu kin jinin Sahyoniyawa suka kai a arewacin birnin Hebron da ke yammacin gabar kogin Jordan, wanda aka ce ya zuwa yanzu an kashe mutane biyu.

A cewar rahotannin farko na yahudawan sahyuniya, mai gudanar da wannan farmakin ya bude wuta kan wata motar ‘yan sanda a daya daga cikin shingayen binciken ababan hawa na sojojin Isra’ila da ke Tarqumiya da ke arewacin Hebron, kuma a cewar ma’aikatar ‘Star of David’ mutane biyu sun samu munanan raunuka sauran sun samu Kananan raunuka, kuma an kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya sun sanar da cewa an kashe wani dan sanda dan shekaru 50 da haihuwa da ke cikin wadanda suka jikkata a wannan samame da aka yi a safiyar yau a arewacin Hebron. Wadannan kafafen yada labarai sun bada labarin kashe ‘yan sanda biyu bayan mintuna kadan.

Ofishin firaministan Isra'ila ya sanar da cewa: Benjamin Netanyahu ba zai halarci bikin bude sabuwar shekara a yau ba saboda yanayin tsaro na musamman biyo bayan ci gaban da aka samu a yammacin kogin Jordan.

Bayan nasarar harin da aka samu na masu kin jinin Sahyoniyawa a yammacin gabar kogin Jordan, inda ya zuwa yanzu aka kashe 'yan sanda biyu, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta aike da dakarun soji da 'yan sanda da dama zuwa yankin.

Rundunar sojin Isra'ila ta yi ikirarin cewa ta gano motar da masu harin na yau suka yi amfani da ita, babu kowa a cikinta, kuma jami'an sun yi nasarar tserewa.

Wannan dai shi ne hari na biyu na masu neman shahada a cikin kwana daya da ya gabata a lardin Hebron da ke gabar yammacin kogin Jordan, wanda ya faru a matsayin mayar da martani ga farmaki da kashe Falasdinawa a yammacin gabar kogin Jordan. A farmakin na jiya mutane 6 da suka hada da wani babban jami'in yahudawan sahyoniya sun jikkata.

................