19 Agusta 2024 - 14:46
Blinken A Ganawarsa Da Shugaban Gwamnatin Sahyoniyawa: Tattaunawar Gaza Na Iya Zama Dama Ta Karshe Don Cimma Yarjejeniya.

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, wanda ya ziyarci yankunan Falasdinawa da aka mamaye, ya gana da shugaban kasar Isra'ila Is’haq Herzog a yau (Litinin) inda ya ce tattaunawar da ake yi dangane da Gaza na iya zama "dama ta karshe" na cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku bisa nakaltowa daga shafin watsa labarai na Quds cewa: Ministan harkokin wajen na Amurka ya yi iƙirari: “Wannan wani muhimmin lokaci ne. Wataƙila ita ce mafi kyau dama ta ƙarshe don dawo da fursunonin gida, da gudanar da tsagaita wuta da sanya kowa a kan kyakkyawar turba don wanzar da zaman lafiya da tsaro".

 Ministan harkokin wajen Amurka ya isa birnin Tel Aviv a daren jiya da nufin tattauna shawarwarin tsagaita wuta a Gaza.

Wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya sanar da cewa, Blinken zai kuma gana da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a ziyararsa ta goma a yankunan da aka mamaye tun farkon yakin Gaza.

 Bayan yankunan Falasdinawa da aka mamaye, sakataren harkokin wajen Amurka zai je Masar domin tattaunawa da mahukuntan kasar da ke shiga tsakani a tattaunawar.