Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku cewa: a
safiyar yau Asabar ne majiyoyin labarai sun bayar da rahoton cewa, sama da
Palastinawa 100 ne suka yi shahada a wani harin da sojojin yahudawan sahyoniya
suka kai kan wata makaranta a birnin Gaza.
Sama da mutane 100 ne suka yi shahada a harin da gwamnatin Sahayoniyya ta kai a wata makaranta da ke unguwar Al-Darraj a tsakiyar Gaza a lokacin sallar asuba.
Wasu mutane da dama kuma sun jikkata a wannan makaranta da ta kasance waje mafaka ta ‘yan gudun hijira.
A wani bangaren kuma, sojojin yahudawan sahyoniya sun yi ikirarin cewa sun kai hari kan wata makaranta a Gaza, wadda ita ce helkwatar dakarun Hamas.
Ya kamata a lura da cewa akalla Palasdinawa 10 ne suka yi shahada a arewaci da tsakiyar Gaza a lokacin hare-haren da sojojin yahudawan sahyoniya suke yi.
Yadda abun ya faru sojojin yahudawan sahyoniya sun yi ruwan bama-bamai a lokacin sallar asuba a wata makaranta da ke unguwar Al-Darj a cikin birnin Gaza, inda akalla Palasdinawa 100 suka yi shahada tare da jikkata wasu da dama. Wanda kimanin Falasdinawa 200 ne ke gudanar da sallar asuba a lokacin da harin da Isra'ila ta kai musu.
